Kwanaki kadan bayan sako daliban kwalejin gandun daji da ke Afakan jahar Kaduna, wadanda su ka shiga tsakani don sakin daliban sun ce akwai yiwuwar sakin daliban Jami'ar Greenfield da ke Kaduna.
Duk da barazanar kama mambobin kungiyar kwadagon da su ka shirya zanga-zanga da yajin aikin gargadi na mako guda, Kungiyar kwadagon ta ce daga daren jiya Lahadi za ta dakatar da komai a Kaduna baki daya.
A kowacce shekara a watan azumin Ramadan, yawancin masallatai a Amurka su na raba abinci ga jama'a a lokacin buda baki. A wannan karon, an raba abincin ne daga cikin mota.
An gudanar da addu'oin neman dauki daga Allah kenan kafin bude bakin Azumin karshe na wannan shekara a masallachin Juma'a na NNPC da ke Kaduna.
Majalisar koli ta addinin islamaa Nijar ta bayyana ganin jinjirin watan Shawwal dake nuna an kamalla azumin Ramadan na wannan shekara.
A yammacin ranar Talata, wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kai hari kan unguwar Jiddari Polo dake garin Maiduguri inda suka dinga harba manya-mayan bindigogi da kuma wasu ababe masu fashewa.
Hukumar kula da ingancin magunguna ta Amurka ta ba da izini ga kamfanin Pfizer da BioNTech na amfani da allurar rigakafin COVID-19 ga yara ƙanana daga shekaru 12 zuwa 15.
Da yammacin ranar litanin nan ne masu aikin ceto suka kammala aikin lalubo mutanen da jirgin ruwan kwale kwale ya kife da su a garin Galkogo dake gaban ruwan Shiroro ta jihar Nejan Nigeria.
Komitin Kula da Harkokin Kudi na Majalisar Dattawa a karkashin Jagorancin Sanata Solomon Adeola ya ce ya gano cewa, a cikin shekaru 5, Ma'aikatu da Hukumomin Gwamnati sun yi sama da fadi da kudade har Naira Triliyan 3 wadanda ba a sa su a cikin lalitar Gwamnati ba.
Matasa daga sassa daban daban na Najeriya sun gudanar da gangamin karbar mulki daga hannun dattawa.
Manoma a Najeriya sunce aikin daminar bana zai fuskanci mummunar barazana fiyeda ta shekarun baya, saboda kalubalen tsaro da kasar ke fama da shi.
Wadansu mazauna birnin Yamai sun koka game da abinda suka kira barazanar da suke fuskanta daga wata sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai karfin Megawatt sama da 80 da aka kafa a tsakar gari ba tare da la’akari da ka’idodin da doka ta shimfida ba.
Sai dai wannan sanarwar da fadar ta fitar, ba ta ambaci laifukan da ake zargi ko tuhumar ake yi wa Hadiza Bala Usman da su ba.
A karon farko bayan sun kwashi kwanaki 100 da kama aiki, shugabanin hukumomin tsaro a Najeriya sun kwashi kusan sa'o'i biyar suna ganawa cikin sirri da daukacin 'yan Majalisar Dattawan kasar kan yadda za a gano bakin zaren da zai taimaka wajen magance matsalar tsaro da kasar ke ta fama da shi.
Gamaiyar yan adawa ta PDP a karkashin jagorancin Shugaban Marasa Rinjaye Enyinanya Abaribe sun baiyana damuwarsu akan yadda Jamiyar APC mai mulki a karkashin shugaba Mohammadu Buhari ta kasa kawo karshen rashin tsaro a kasa, wanda shi ne muhimmin dalilin Kampe din su a shekara 2015.
Domin Kari