Kungiyar kwararru mai fafutukar daidaita lamurran zamantakewar al’umma ‘yan kabilar Igbo mai suna, Nzuko Umuna, na neman babban sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya janye umarnin sa na jami’an ‘yan sanda su kashe duk wani dan haramtaccen kungiyar IPOB.
A jiya Litinin jami’an sojan kasar Mali suka tsare shugaban kasa da Firai Minista da kuma ministan tsaro na gwamnatin wucin gadi.
Yayin da Jami’an kiwon lafiya ke ci gaba da kula da fiye da mutane 70 da hadarin gobara ya ritsa da su a gidan sayar da man fetir na Al-ihsan dake kan titin Sharada a birnin Kano, hukumomin kashe gobara a jihar na danganta lamarin da rashin kiyaye ka’idoji daga bangaren mamallaka gidan man.
A Najeriya ana ci gaba da samun salwantar rayuka sanadiyar ayukkan ‘yan bindiga lamarin da masana ke kallon cewa shawo kansa ya gagari hukumomi.
Dubun wadansu mahara masu garkuwa da mutane ta cika a garin Garu a karamar hukumar mulkin Illela ta jihar Sokoto da ke iyaka da Birni N'Konni a Jamhuriyar Nijar, yayin da wadansu suka kashe mutun guda a Araba dake da tazarar kilomita 2 da birni N'Konni.
Majalisar Dattawan Najeriya ta na duba yiwuwar yi wa dokar rigakafin ta'addanci ta shekara 2013 kwaskwarima inda za a hana biya da karbar kudin fansa.
Wasu mahara dauke da manyan bindigogi akan babura, sun kashe Sardaunan Kontagora tare da wasu mutane a jihar Neja dake arewacin Najeriya.
Hukumar Shige da Fice ta ce ta kafa takunkumi da bayar da faspo ga masu bukata a dukkanin Ofisoshinta da ke kasar har sai ranar 1 ga watan 6 Yuni.
Shugaba Mohammadu Buhari ya aika wa Majalisar dokokin Najeriya wata takardar neman izinin ya sake karbo bashin dalar Amurka biliyan 6.18 daga kasashen waje da manyan cibiyoyin hada hadar kudade na duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga kasashen Turai da cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da su yi la’akari da rage illar da cutar Coronavirus ke yi wa tattalin arzikin Afirka ta hanyar sake fasalin sassan basussukan domin samun sauki gaba daya.
An kashe Sojojin Najeriya guda uku a wani hari da wasu 'yan bindiga su ka kai a jihar Neja dake Arewaacin kasar.
Tsokacin na zuwa ne a daidai lokacin a ci gaba da kai hare-hare da Isra'ila da Hamas ke yi wa junansu, wadanda suka yi sanadiyyar asarar rayukan fararen hula a bangarorin biyu.
Duk da barazanar kama mambobinta a jihar Kaduna, kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta fara zanga-zangar gargadi ga gwamnatin jihar game da korar ma’aikatan da ta yi.
Kungiyoyi agaji na taka rawa wajen samar da makoma ga kananan yara da basu da hanyar samun ilimi.
Domin Kari