Kasar Burtaniya ta ce za ta taimakawa Najeriya don ganin cewa ta fita daga matsalolin rashin tsaro da suka dabaibaiye kasar musamman yankin arewa.
A Najeriya Majalisar Dattawa ta amince da daidaita mataki tsakanin masu digiri daga Jami'oi da masu takardar babbar difloma wacce aka fi sani da HND a turance.
“Matsainacin halin take hakkin yara da ake yi a duk fadin Tigray bai nuna alamar raguwa ba, kusan watanni bakwai ke nan tun lokacin da fada ya barke a arewacin Habasha.
Jerin masu gabatar da shaidu sun kammala bayar da ba’hasi ranar Jumma’a, inda su ka yi ta bayyana yadda aka yi ta tafka almundahana, da kama mutane ba bisa ka’ida ba.
Kimanin mutum 18 wasu mahara suka kashe yayin da 15 suka jikkata a garin Beri dake cikin jihar Nejan Najeriya.
A karshen makon jiya ne wa’adin mulkin shugabannin kananan hukumomin jahar Nasarawa ya kare suka kuma mika mulki wa daraktocin ma’aikatan kananan hukumomi goma sha uku na jahar.
Majalisar Wakilan Najeriya na shirin yin dokar da za ta soke shirin yi wa kasa hidima, NYSC bisa dalilin tabarbarewar Tsaro a kasar.
Hukumomi a Jihar Imo, sun yi bayani game da kashe tsohon mai bai wa tsohon shugaba Goodluck Jonathan shawara kan harkokin siyasa Ahmed Ali Gulak, wanda wasu 'yan bindiga suka yi a safiyar jiya Lahadi.
A ranar Litinin na karshen watan Mayu, Amurkawa kan karrama Sojojin da suka rasa rayukansu yayin aikin bautan kasarsu. Lokaci ne na tunawa da sadaukarwar da wasu kalilan suka yi domin amfanar da yawa, da yaba da bautar su wajen kare kasar da manufofinta.
'Yan mata a jihar Kano da ma sauran jihohin arewacin Najeriya na fuskantar matsanaci tsangwama daga bangaren samari dangane da sanya abaya da ta shigo kwanan nan.
A ranar 17 ga Mayu, Amurka ta ayyana ƙungiya guda da mutum 16 waɗanda ke da alaƙa da gwamnatin. Kungiyar ita ce Majalisar Gudanarwar kasa, ƙungiyar da mulkin soja ta kirkira don tallafawa juyin mulkin tda ta yi ba bisa doka ba.
A kokarin yaki da 'yan bindiga da suka addabi jihar Nejan Najeriya, gwamnatin jihar ta kaddamar da wata rundunar sintiri da ta baiwa horo na musamman ta yadda za ta yi yaki da wadannan 'yan bindiga.
Duk da cewa AQAH tana ikirarin yi wa mutanen Lebanon hidima, gaskiyar maganar ita ce suna aika kudade ta haramtacciyar hanya zuwa asusun ajiya, inda suke saka cibiyoyin kudaden Lebanon cikin hadari a saka masu takunkumi.
Daliban Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha, da ke Ijero-Ekiti a ranar Laraba sun yi zanga-zanga bayan da abokan karantunsu su kimanin 100 suka suma sanadiyyar shakar wani sinadari.
Matsalar rashin tsaro a Najeriya na ci gaba da haifar da damuwa da tilasta jama'a daukar matakai koda basu da dadi a rayukan su.
An shiga rana ta uku da zaman zullumi a kayuka da garuruwatakwas na yankin karamar hukumar Kirikasamma ta a jihar Jigawa dake yamma maso arewacin Najeriya biyo bayan rikici Tsakani manoma da Fulani makiyaya a yankin.
A yau a ke sa ran tattara ra'ayoyin 'yan Najeriya game da gyaran fuska cikin dokokin tsarin mulkin kasar da a ke ganin akwai bukatar sake duba wadannan dokokin.
Domin Kari