A Najeriya mahukuntan kasar na shirin sabunta jadawalin yawan jama'an kasar saboda Hukumar Kidayar Jama'a ta Kasa ta ce ta fara daukan matakai kuma tuni har ta riga ta tura ma'aikatan ta fili domin su kasafta kasar tun daga gundumomi domin a samu a yi kidayar a shekara 2022.
Amurka ta damu ainun game da barazanar da ake yi wa yankin Habasha. Babban mahimmanci a cikin waɗannan barazanar shine rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Tigray na ƙasar.
Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban Islamiyyar Salihu Tanko 148 a garin Tegina ta Karamar Hukumar Rafin jihar Nejan Nigeria sun ce sai an biya Naira miliyan 150 a matsayin kudin fansa kafin su sako yaran da akasarinsu yan kasa da shekaru 13 ne.
A Najeriya, wata kungiya mai zaman kanta da ake kira 'Love Love Foundation', kuma mai rajin kare hakkin bil adama, ta shigar da kara a kotun ECOWAS inda ta kalubalanci dakatarwar da gwamnatin Najeriya ta yi na ayyukan Twitter a kasar.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya gana da shugabanin kungiyoyin fararen hula a fadarsa inda suka tantauna kan,wasu mahimman batutuwan da suka shafi tafiyar kasa a ci gaba da neman hanyoyin magance matsalolin da aka yi fama da su a baya.
Dubun dubatar fararen hula a Sudan sun gudanar da tarukan gangami a Khartoum domin cika shekaru biyu da fatattakar da sojoji suka yiwa masu rajin dimokradiya, suna neman adalci ga ‘yan uwansu da aka kashe ranar 3 ga watan Yunin 2019, a fatattakar.
Wasu mahara sun kashe mutane 88 a jihar Kebbi, Najeriya a ranar Alhamis, abin da ya ja hankalin gwamnan ya yi alkawarin tura karin jami’an tsaro yayin da rashin tsaro ya ci gaba da yaduwa ba tare da kulawa ba a yankin arewa maso yammacin kasar.
Jakadar kasar Amurka Mary Beth Leonard ta ce kasar Amurka na tare da Najeriya a wannan lokaci na kalubalen tsaro kuma zata bada gudumawa wajen ganin an shawo kan matsalar ta fanoni daban daban.
Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken ya yi balaguro zuwa Isra’ila kwanan nan don yin aiki kan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza. Sakatare Blinken ya ce: "Hakan zai fara ne da amince cewa an yi asara daga bangarorin biyu da yawa."
Amurka da Tarayyar Turai sun nuna damuwa kan shawarar da Najeriya ta yanke na dakatar da amfani da Twitter bayan da katafaren kamfanin sada zumunta na Amurka ya goge wani sako daga shafin shugaba Muhammadu Buhari saboda keta dokokinsa.
Gwamnatin kasar Burkina Faso ta ce adadin mutanen da suka mutu daga mummunar harin da ‘yan bindiga suka kai ya karu zuwa 132, bayan da wasu mahara dauke da makamai suka kai farmaki cikin dare a wani kauye da ke fama da kaifin kishin Islama a arewa maso gabas.
A Najeriya bayan ibtila'in da ya yi sanadiyar salwantar rayuka sama da 100 a jihar Kebbi gwamnatin jihar ta ce za ta hada hannu da gwamnatin jihar Neja don gano musabbabbin wannan ibtila'in da kuma daukar matakan kaucewa sake faruwar irin sa.
Faransa ta fada a ranar Alhamis cewa za ta dakatar da ayyukan soji na hadin gwiwa tare da sojojin Mali bayan juyin mulkin da kasar ta yammacin Afirka ta yi a karo na biyu cikin wata tara.
Tsawon yajin aikin ma'aikatan sashen shari'a a Najeriya ya kawo koma baya ga lamuran adalci don yadda rashin zaman kotuna ya bar wadanda a ke tuhuma da dama a gidajen yari ko ofisoshin 'yan sanda.
A cikin makonnan ne Gwamnatin Jihar Borno ta rufe wasu sansanonin 'yan gudun hijira biyu dake cikin garin Maiduguri cikin 27 da ake da su, inda tayi jigilar 'yan gudun hijiran zuwa wani kauye da ake kira Auno dan tsugunanar da su a wasu rukunin gidaji da ta gina guda 580.
Hukumar Makarantar Islamiyyar Salihu Tanko, dake garin Teginan Jihar Nejan Najeriya da 'yan bindiga suka yi garkuwa da dalibanta a ranar Lahadin da ta gabata, ta tabbatar da mutuwar 2 daga cikin iyayen daliban sakamakon tashin hankalin sace masu 'ya'ya.
Domin Kari