Da misalin karfe 8:24 na safe yayin da jirgin kasa ya isa wata tashar karkashin kasa, a unguwar Sunset Park, mutumin da ke sanye da karamar rigar masu aikin gine-gine, wanda ya rufe fuskarsa da abin tare iska mai guba, kafin ya fara bude wuta a kan mutanen dake cikin jirgin da wasu dake kusa da jirgin, inji kwamishinar ‘yan sandan birnin New York, Keechant L. Sewell
Harbin kan mai uwa da wabin ya haifar da fargaba da tashin hankali a cikin jirgin. Wannan abu na faruwa ne a daidai lokacin da ake fama da yawan harbe-harbe a fadin birnin da kuma karuwar miyagun ayyukan a tashar jirgin kasa na karkashin kasa, lamarin da ke tsorata mutanen birnin da suka fara komawa ga amfani jirgin bayan lokacin annoba da shiga jirgin ya yi kasa.
Maharin ya arce daga wurin kuma har iyau ba a gano shi ba a cewar jami’an ‘yan sanda. Suka ce har iyau ba a iya bayyana fuskarsa ga jama’a ba. Wani babban jami’in bincike ya ce an ga bindiga a tashar jirgin.
Ku Duba Wannan Ma Hari a New York: Mutane Biyar Na Nan Rai Kwakwai, Mutu KwakwaiJami’in ya ce dan bindigan ya tuko mota ce da ya yi hayarta daga kamfanin U-Haul ya shigo New York.
Sai dai Mr. Adams tsohon keftin din ‘yan sanda, ya ki yin karin bayani a kan inda binciken maharin ya kai a wannan lokacin. Ya ce “wannan wani lokacin ne mai muhimmanci.” “Muna so mu ci gaba da rike muhimman bayanan ne saboda kada mu bada kofa ga mutumin da muke nemansa,” inji Adams
Ma’aikatar kwana-kwana ta ce mutane biyar na cikin mawuyacin yanayi amma babu wanda rauninsa ke barazana ga rayuwarsa.
Gwamnar jihar New York Kathy Hochul ta shawarci ‘yan New York da su kasance “a farke da lura,” tana mai cewa "wannan yanayin harbi ne da har yanzu ake fama da shi a cikin birnin New York."