Tsohon Madugun ‘Yan Tawayen Laberiya Prince Johnson Ya Mutu Yana Da Shekaru 72

Prince Johnson

Johnson ya kasance cikin jagororin masu adawa da kafa kotun da za ta saurari kararrakin dake alaka da laifuffukan yakin da aka aikata lokacin yakin basasar Laberiya.

Tsohon madugun ‘yan tawayen Laberiya Prince Johnson, jigo a yake-yaken basasar kasar da suka faru bi da bi tsakanin 1989-2003, ya mutu a yau Alhamis yana da shekaru 72, kamar yadda jami’an jam’iyyarsa da na Majalisar Dattawan kasar suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Daga bisani, Prince Johnson, wanda ya fito daga yankin Nimba na arewacin kasar, ya zamo mai wa’azi karkashin Majami’ar Evengelical inda ya samu shahara.

Ya kuma kasance cikin jagororin masu adawa da kafa kotun da za ta saurari kararrakin dake alaka da laifuffukan yakin da aka aikata lokacin yakin basasar Laberiya.

“Kwarai, mun rasa shi da safiyar yau. Ya mutu a asibitin “Hope for Women”,” kamar yadda Wilfred Bangura, babban jami’i a jam’iyyar Prince Johnson ta “Movement for Democracy and Reconstruction Party”, mai rajin kafa dimokradiyya da sake gina kasa, ya shaidawa AFP.