Tinubu Zai Yi Wa Majalisar Ministoci Garanbawul - Fadar Shugaban Kasa

  • VOA Hausa
Mashawarcin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da haka ga maneman labaran fadar shugaban kasa a yau Laraba a fadar ta Aso Villa, dake Abuja.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana bukatar yin garanbawul a majalisar ministocinsa.

Mashawarcin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya tabbatar da haka ga maneman labaran fadar shugaban kasa a yau Laraba a fadar ta Aso Villa, dake Abuja.

Ya kara da cewa sabanin rade-radin da ake yi, gwamnati mai ci ta samu dimbin nasarorin a kokarinta na kawo sauye-sauye a fannin tattalin arziki, wadanda galibin al’umma basu da masaniya akai.

Onanuga ya cigaba da cewar Tinubu ya umarci ministocin akan su tabbatar sun mu’amalanci jama’a ta hanyar yayata ayyukan da gwamnati ke gudanarwa a ma’aikatansu.

An ruwaito yana cewa, “ni ban bada wani wa’adi. Shugaban kasa ya bayyana bukatarsa ta gudanar da garanbawul a majalisar ministocinsa kuma zai aiwatar da hakan. Ban sani ko yana nufin aiwatar da hakan kan nan da ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa ba, amma tabbas zai aiwatar.”