Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan sojoji 47 da ‘yan ta’adda suka kashe a kauyen Gorgi da ke jihar Borno.
Ya ce “ba za mu taba barin kokarin da sojojinmu suka yi ya tafi a banza”.
Ya kuma kara da cewa, dalilin da ya sa mutuwar kowane soja ke yi masa ciwo shi ne saboda ya san mene ne zama soja ya kunsa.
A yanzu dai rundunar sojin kasar ta aika wata tawaga domin gudanar da bincike kan lamarin.
Manjo Janar John Enenche na rundunar tsaron kasar ya yi wa manema labaru karin haske, kuma ya ce abin da ya faru wasu sojoji ne suka shirya kai dauki ga wasu mayakan yayin da aka yi masu kwanton baunar.
Ya kara da cewa 'yan ta'addan sun yi ta harbe-harbe ne a kan motar da ke dauke da kayan yaki na manyan bindigogin Artillery da bama-bomai, wanda dalilin hakan kayan fadan suka fashe.