Makarantu biyu rundunar sojojin ta sauyawa gurabe da zummar kara karfafa tsaro a arewa maso gabashin Najeriya.
Makarantar dake horas da yaki da ta'adanci dake Kontagora a jihar Neja an dauketa an mayar da ita Buni Yadi a jihar Yobe. Haka ma aka dauke makarantar injiniyoyi dake Makurdi a jihar Benue zuwa Biu a jihar Borno.
Daraktan watsa labarai na hedkwatar rundunar Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya bayyana dalilin yin hakan. Yace sun maida makarantaun ne inda ake yaki da ta'adanci. Inji Kanar Sani ta Buni Yadi ne 'yan ta'adan suke fitowa daga dajin Sambisa kana su shiga wasu wurare. Kafa makarantar a Buni Yadi zai hana 'yan ta'adan zuwa wasu wurare.
Horas da sojoji a wurin zai basu damar sanin yanayin yankin sosai. Haka ma makarantar da aka kai garin Biyu zata tabbatar da zaman lafiya da kawar da duk wani sabani.
Masana harkokin tsaro irin su Air Commodor Ahmed Tijjani Baba Gamawa suna maraba lale da wannan matakin.Yace dole na dakarun Najeriya su tsaya su kware su san yadda za'a murkushe miyagun mutane kamar 'yan Boko Haram.Abun da Janar Buratai ya yi yanada kyau, inji Gamawa.
Shi ma Manjo Janar Yakubu mai ritaya yace shin inda aka kai daliban akwai duwatsu da ruwa da hamada da zasu tayasu samun horan da suke bukata? Idan akwai babu laifi a canza masu gurabe.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5