Mataimakin ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rasha Serge Ryabkov yace mai yiwuwa ne Moscow ta rama matakin da Amurka ta dauka na kakaba mata wadansu jerin sababbin takunkumi a matsayin ladabtarwa sabili da shish-shigin da Rasha tayi a zaben shugaban kasa da aka gudanar bara.
‘yan Jam’iyar wakilan Amurka sun amince da kudurin jiya Talata, wanda kuma ya fadada sa idon majalisa kan ikon Shugaba Donald Trump na janye takunkumi.
Bisa ga cewar kafar watsa labaran kasar Rasha, Ryabkov ya yi gargadi da cewa, sababbin takunkumin zasu gurgunta damar inganta dangantaka tsakanin Moscow da Washington. Ya kuma ce Rasha ta gargadi gwamnatin Trump a lokutan baya cewa, zata maida martani idan ‘yan majalisar dokokin amurka suka amince da kudurin.
An amince da sabuwar dokar sawa shugaban kasar ido ne bayan an shafe sama da wata guda ana tattaunawa ba tare da banbancin siyasa ba. Kudurin farko ya sami gagarumin rinyaje a majalisar dattijai inda sanatoci casa’in da bakwai suka kada kuriar amincewa biyu kuma basu amince ba.
Kudurin da majalisar wakilai ta amince da shi ya sami goyon bayan ‘yan majalisa dari hudu da goma sha tara, uku kuma basu amince ba, sannan ya hada da kakabawa Iran da Koriya ta Arewa takunkumi, da kuma takunkumin ladabtarwa da aka kakabawa Rasha bisa dalilai dabam dabam.