A cikin wasikar da aikawa Modi a ranar Juma’a, ya masa barka game da zabensa a karo na biyu a matsayin Firai minista. Khan ya rubuta cewa Pakistan tana so a magance duk wata matsala, ciki har da batutuwa masu nasaba da takaddamar yankin Kashmir, a cewar kafofin yada labarai.
Khan ya kara da cewa tattaunawa tsakanin kasashen biyu, itace hanya daya tilo da zata taimakawa kasashen su yaki talauci, a don haka dole ne su yi aiki tare domin ci gaban yankin.
Pakistan tana bukatar tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin Asia ta Kudu a cewar wasikar Khan, yana mai fadin cewa dole ne a samu haka kafin kasashen da ma yankin su ci gaba.
Sai dai jami’an India sun ce Modi bai shirya wata ganawa da Khan a taron kolin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Turai da Asia a Bishkek babban birnin kasar Kyrgyzstan a mako mai zuwa.
A iya sani na babu wata ganawa da aka shirya tsakanin Firai Minista Modi da takawarar aikinsa na Pakistan Imran Khan a gefen taron kolin, inji mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen India, Raveesh Kumar.
A ‘yan shekaru da suka shude, India taki amincewa da duk wani shirin tattaunawa, tana mai cewa sai an kawo karshen ta’addancin kan iyaka kafin fara wata tattaunawa.