Lamarin ya kai ga har sai da shugabannin al’ummar Afurka su ka yi kira ga iyaye da su maida hankali wurin kula da tarbiyyar ‘ya’yansu da kuma mu’amala da suke yi da sauran yara.
Tun a shekarun baya rahotannin jami’an tsaro su ka nuna ana ci gaba da kama matasa bakaken fatar Amurka da Latino fiye da takwarorinsu farare da na Asiya, amma wani abin mamaki shi ne matasa da iyayensu suka fito daga nahiyar Afurka sun fara aikata laifuka masu yawa a birnin New York.
Rahotannin ‘yan sanda sun nuna ana samun irin wadannan matasa na Afurka da dama na aikata laifin, inda a bara wani matashi da iyayensa suka fito kasar Gambiya ya kashe mahaifiyarsa saboda tana masa fada ya rabu da abokan banza ya nemi sana’a.
Shi ko Sarkin Musulmin na New York, Alhaji Yahuza Abubakar ya ce iyaye na da muhimmiyar rawa da ya kamata su taka wurin tarbiyyar ‘ya’yansu.
Shi ma Muhammad Bashir Kabore, mataimakin shugaban kungiyar Yankasa da ta hada Ghana, Najeriya, Gambiya, Nijer da sauransu, ya ce akwai bukatar sanya idanu a kan kai-komon yara.
Sai dai shugabanni a fannin cigaba sun gabatar da sauye-sauye na shari'ar laifuka da aka yi niyya don gyara rashin daidaituwar Bakar fatar Amurkawa da aka kama, aka yanke musu hukunci da tsare su. Amma a aikace, a garuruwa irin su New York, wadannan sauye-sauyen sun ci tura, lamarin da ya haifar da yawaitar aikata laifuka, inda aka ci zarafin bakar fata Amurkawa tare da tsare su, a cewar masana.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5