Kididdiga na nuni da cewa, kusan rabin al’ummar Najeriya mata ne kuma kashi 20 daga cikin su na fama da nakasa, a cewar wani bincike da wata kungiyar raji ta yi. ‘Yan raji sun ce galibin wadannan matan na fuskantar wariya da kyama da kuma rashin adalci saboda yanayin da suke ciki, har ma da tashin hankalin cin zarafi. Amma wata mata mai larura ta musamman na daukar matakin tabbatar da cewa mata kamar ta sun sami dama a bangaren kiwon lafiya kuma ana yi masu adalci.
Eberendu Onyinyechi ta yi fama da wata rashin lafiya da ta shanye kafafuwan ta a lokacin da take kasa da shekara daya da haihuwa.
Duk da haka, yanayin rashin lafiyarta bai taka mata burki ba, ta yi ilimi har matakin digiri, yanzu kuma ta na aiki da gwamnatin Najeriya. Amma kamar sauran mata masu nakasa, Eberendu ta ce ta fuskanci cin zarafi.
Mata da yara mata masu nakasa a Najeriya na tattare da hadarin da ya shafi cin zarafi na jinsi fiye da maza ‘yan uwansu, a cewar wata kungiyar raji mai zaman kanta.
A shekarar da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta sanya hannu a wata doka ta inganta rayuwar masu nakasa. Amma ‘yan raji sun ce rashin ilimi, da rashin samun dama, da talauci na ci gaba da kawo wa mata masu nakasa cikas a bangaren samun adalci