Lauyan mai kwarmaton nan da ya nuna matukar damuwa game da wayar tarho da shugaba Trump ya yi da shugaban Ukraine, wanda ya janyo kafa wani kwamitin bincike da Majalisar Wakilai ta yi na yiwuwar tsige Trump ya ce mutumin da yake wakilta ya amince zai bada amsar tambayoyin 'yan jam'iyyar Republican a rubuce.
Lauya Mark Zaid ya rubuta a kafar Twitter jiya Lahadi cewa mai kwarmaton zai amsa tambayoyi daga ‘yan jam’iyyar Refublikan “A rubuce, bayan sharadin rantsuwa da kuma zartar da hukunci idan an yi karya."
Zaid ya kara da cewa tambaya kadai da, ita ko shi, ba zai amsa ba ita tambayar saninsa ko saninta.
Zaid ya ce wasu ‘yan jam’iyyar Refublikan suna “kokarin su bayyana wanda mu ke wakilta wanda hakan zai iya barazana ga tsaron sa tare kuma da iyalansa ….. kuma zama mai kwarmata bayanai ba wai aiki ne na bangaranci ba ko yinkurin tsigewa ba. Wannan ba aikinmu ba ne.
Zaid ya mika goron gayyatarsa zuwa ga dan majalisa, David Nunes, babban dan jam’iyyar Refublikan a kwamitin ayyukan leken asirin Majalisar wakilan Amurka, daya daga cikin ‘yan kwamitin da suke sauraron ba'asin yiwuwar tsige Trump, Nunes har yanzu bai bada amsa ba.