Hatsarin kwale-kwalen daya afku da safiyar yau Juma’a a bangaren Dambo zuwa Ebuchi na kogin Neja, ya yi sanadiyar asarar rayuka da dama.
A cewar shaidun gani da ido, kwale-kwalen mallakin wani mai suna Musa Dangana na dauke da fiye da fasinjoji 200, ciki har da mata ‘yan kasuwa da leburorin dake aiki a gonaki, a kan hanyar ta zuwa kasuwar Kdake ci mako-mako a jihar Neja.
Kwale-kwalen ya kife tare da jefa dukkanin wadanda ke cikinsa a ruwa.
Ana ci gaba da aikin ceto inda masu ninkayar yankin ke kokarin lalubo gawawwakin wadanda al’amarin ya rutsa dasu.
Lokacin hada wannan rahoto, an tsamo gawawwaki 8, yayin da ake ci gaba da aikin lalube da ceto domin gano ragowar fasinjojin.
Ku Duba Wannan Ma Kwale-Kwale Ya Kife Da Mutum 300 A Neja
Ku Duba Wannan Ma Lodi Fiye Da Kima Ne Ya Haddasa Hatsarin Jirgin Ruwa A Kogin Neja - Hukumomi
Mummunan hatsarin na zuwa ne ‘yan watanni bayan afkuwar makamancinsa a kogin Muwo Gbajibo dake karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja a ranar 1 ga watan Oktoban da ya gabata, al’amarin da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dama.