Karin Takunkumi Kan Gwamnatin Mulkin Soji Ta Kasar Burma

资料照:美国国务卿布林肯

Amurka ta sanar da karin takunkumi kan gwamnatin mulkin soji ta kasar Burma. Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya hambarar da zababbiyar gwamnatin dimokiradiyya a watan Fabrairu, gwamnatin mulkin soji ta mayar da martani mai karfi ga masu zanga-zangar kare demokradiyya, inda aka kashe sama da mutum 800, ciki har da yara, tare da tsare dubbai.

A ranar 17 ga Mayu, Amurka ta ayyana ƙungiya guda da mutum 16 waɗanda ke da alaƙa da gwamnatin. Kungiyar ita ce Majalisar Gudanarwar kasa, ƙungiyar da mulkin soja ta kirkira don tallafawa juyin mulkin tda ta yi ba bisa doka ba.

Goma sha uku daga cikin mutanen manyan mukarraban gwamnatin soja ne kuma uku manyan yaran hafsoshin soja da aka nada a baya ne.

Sakamakon ayyanawar, duk kaddarori da abubuwan da suke da shi a cikin Amurka an rufe su. Haka kuma, sai dai idan an ba da izini, duk ma'amaloli da Amurkawa ke yi a cikin Amurka wanda ya shafi dukiyar waɗanda aka ayyana an hana su.

Su ma kasashen Burtaniyya da Canada sun sanya nasu takunkumi dangane da juyin mulkin da ke faruwa a Burma.

A cikin wata sanarwa, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya rubuta, “Kamar yadda Shugaba Biden ya bayyana, Amurka za ta ci gaba da ganin cewa wadanda suka yi juyin mulkin sun dauki alhakin abin da suka yi.

Matakin da muka dauka a yau, na nuna muhimmancin abin da mu da kawayen muka sa gaba, na tursasa hukumomin kasar ta fuskar siyasa da hanyoyin hada-hadar kudade, muddin bas u daina cin zarafin mutane ba, ko kuma ba su dauki matakin mutanta ra’ayin mutane.”

Sakatare Blinken ya ce Amurka da kawayenta na G7 suna maraba da shirin yarjejeniya guda biyar game da Burma wanda taron Shugabannin kungiyar ASEAN suka kafa a karshen watan Afrilu.

Wannan shirin ya bukaci dakatar da tashin hankali nan da nan; samar da masi shiga tsakanin ba tare da bata lokaci ba, samar da tallafi don agaza al’umar kasar daga kungiyar ASEAN, sannan sai ziyarar mai shiga tsakani na musamman da tawagarsa, don ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a kasar.

Mista Blinken ya bukaci gwamnatin soja ta Burma da ta hanzarta ba tare da wani sharadi ba, ta ba da hadin kai ga kungiyar ta ASEAN da Majalisar Dinkin Duniya don aiwatar da wannan shirin.

Sakataren Gwamnati Blinken ya ce, "Abin takaici," har yanzu gwamnatin mulkin soja ta ki ba da hadin kai ta hanyar da ta dace kuma ba ta yin wani yunkuri na maido da Burma kan turbar dimokiradiyya, inda ta ci gaba da nuna danniya da muzguna wa mutanenta. "

Amurka na kira ga dukkan kasashe, da su duba yiwuwar saka takunkumi akan gwamnatin sojin da ke Mulki, a wani mataki na dora alhaki akansu, dangana da juyin mulkin da cin zarafin bil adama da ake yi, don a kauwcewa karuwar tashin hankali.