Hanyar Samun Zaman Lafiya A Kasar Habasha

FILE PHOTO: Ricikin kasar Habasha

Yayin da ‘yan Habasha a fadin duniya ke jiran ganin ko yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma, mai sarkakkiya za ta yi aiki, wani gungun ‘yan kasar mazauna kasashen ketare ya hallara a nan hedikwatar Muryar Amurka da ke birnin Washington don tattauwa kan batun.

Shirin, mai taken “Habasha: Hanyar Samun Zaman Lafiya” wanda aka yada ta gidan talabijin, ya tara ‘yan raji da dama, da kwararru da dai sauransu daga kabilu daban daban na Habasha, saboda su samu damar da ba su saba samu ba, ta yin magana kan tashin hankalin da aka shafe wajen shekaru biyu ana yi, wanda har ya daidaita kasar.

Mahalarta sun ce ana matukar bukatar tattaunawa ta tsakani da Allah irin wannan. “Muddun ana so a wuce zancen banbance banbancen kabilu, akwai bukatar yin muhawara da tattaunawa don a fayyace komai,” a cewar daya daga cikin masu jagorantar taron, Etana Habte, wanda wani manazarci ne dan asalin Habasha, wanda ya kware kan tarihin siyasar Habasha da ma kuryar Afurka baki daya.

Da take magana ga mata Meaza Gebremedhin, yar gwagwarmayar Tigrai, mai bincike kuma mai fafutukar kare hakkin dan Adam, na daya daga cikin mahalarta taron. Tun bayan barkewar yaki a yankin Tigray na kasar Habasha, ta shirya zanga-zangar kuma ta yi magana game da cin zarafi a kasarta.

An yi mata barazanar kisa, kuma wani ma ya taba nuna mata bindiga a yayin wani gangami a Los Angeles, amma ta ce babu shakka idan aka kwatanta da munin da ya faru a yankin Tigray.

"Ba kawai muka ji labarin yadda yakin ya yi muni ba, mun rayu cikinsa ne," in ji ta.