Wata kungiyar kare hakkin bil’adama, ta ce akalla mutane 140 aka kashe a jihar Oromo da ke kasar Habasha ko kuma Ethiopia, a lokacin da jami’an tsaro suka far ma wasu masu zanga zangar kin jinin gwamnati.
Wannan adadi dai ya haura wanda hukumomin kasar suka fitar.
A yau juma’a, Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce, mutane 140 aka kashe kana aka jikkata wasu da dama, a arangamar da kungiyar ta ce ita ce mafi muni da ta samu kasar tun bayan shekarar 2005 da aka yi rikicin zabe.
Wannan adadi da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar ya ninka har sau biyu adadin da aka fitar a watan da ya gabata.
A baya gwamnatin kasar ta ce mutane biyar ne kacal suka mutu.
Zanga zangar ta samo asali ne bayan da wasu suka nuna adawarsu kan wani shirin gwamnati na yin gine-gine a wasu gonaki da ke wajen Addis Ababa, babban birinin kasar.