A yau Jumma’a mata sun yi ta wake-waken cewa suna bukatar a basu kashi hamsin cikin dari na mukamai a lokacin da daruruwan su daga jihohin kasar talatin da shida, ciki har da birnin tarayya suka yi wani jerin gwano daga dandalin Eagle Square zuwa kofar majalisar dokokin Najeriya a birnin na Abuja a karkashin wata hadakar kungiya mai suna Coalition of Women Groups.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar Binta Kasimu, ta ce sun zo majalisar ne domin su bayyana bukatun su na neman mukamai, kuma a ganinta mata sun cancanta tun da dama cancanta a ke so ba dauki-dora ba.
Ita kuma tsohuwar shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa Madam Evelyn Onyilo, ta ce har yanzu a Najeriya babu mata da suka kai kashi talatin da biyar cikin dari, saboda haka dole ne a yi adalci a nada mata sha shida a gwamnati mai jiran gado.
Maryam Aliyu Abdullahi, daya daga cikin wadanda suka yi tattakin, ta ce sun zo majalisar ne domin a nan ne suke da wakilan da zasu ji kukan su, ta kuma nemi wakilan su dube su da idon rahama a ba su abinda ya dace.
A cewar Aishatu Adamu, mata suna da ilimi da ta ke ganin ya ma fi na maza, tun da su ma mata suna da kwararrun likitoci da injiniyoyi, da farfesoshi, kuma hasali ma mata ne iyayen duniya. A saboda haka idan aka ba namiji mukami daya, ita ma mace a bata, a yi raba daidai.
A wata kididdiga da kungiyar kwadago ta duniya da ake kira ILO a takaice ta yi, ya nuna cewa mata suna baya a yawan ma'aikata a duniya da biliyan daya da miliyan dari uku sabanin maza da suka kai biliyan biyu.
Ga karin bayani cikn sauti daga Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5