Ya ce labarai ne na bogi da kuma karya da aka shirya don bata nasarorin diflomasiyyar da Burundi ta yi na baya-bayan nan da kuma karfafa demokradiyya.
Agathon Rwasa na babbar jam'iyyar adawa ta National Congress ya fadawa Muryar Amurka cewa gwamnatin Burundi na kame magoya bayan 'yan adawa a duk lokacin da aka kai harin bam a Bujumbura ko lardunan.
Willy Nyamitwe, shugaban sashin yada labarai da sadarwa a fadar gwamnatin Burundi, ya gaya wa wakilin Muryar Amurka James Butty cewa shugaban ‘yan adawa Rwasa ya ji kunya da wadannan nasarorin.
Nyamitwe ya ce hakkin gwamnati shi ne ta kare ‘yan kasarta, ba ta sace su ba.
A wani bangaren kuma, Shugaban kasar Tanzania Samia Suluhu Hassan za ta fara ziyarar kwanaki biyu a kasar Burundi a ranar Juma’a (16 ga watan Yulin).
Nyamitwe ya ce ziyarar za ta karfafa alakar da ke tsakanin Burundi da Tanzania.