An Fara Shari’ar Mutuwar Mutum 135 A Turmutsutsun Kallon Kwallon Kafa Na Indonesiya

Mutanen da suka mutu a tashin hankalin filin kwallon kafa na Indonisiya

Wata kotu a kasar Indonesiya ta fara shari'ar wasu mutane biyar bisa zargin sakaci da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 135 a cunkoson filin wasan kwallon kafa.

Tun farko dai ‘yan sanda ne suka harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa hartsigi da ya barke, lamarin da ya haddasa firgicewar tarin ‘yan kallon cikin tirmutsutsu aka murkushe mafi yawa daga cikinsu yayin da suke neman hanyar ficewa.

Mummunan tashin hankalin na ranar 1 ga Oktoba ya faru ne a birnin Malang na Gabashin Java, ya kasance daya daga cikin bala'o'in wasanni mafi muni a duniya. Jami’an ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa lokacin da yan kallo suka mamaye filin wasa, bayan da Arema FC ta sha kashi a gida a karon farko cikin shekaru 23 daga abokiyar hamayyarta Persebaya Surabaya.

Wasan da aka yi a filin wasa na Kanjuruhan, ya samu halartar magoya bayan Arema FC ne kawai, domin masu shirya gasar sun haramtawa magoya bayan Persebaya, saboda tarihin wasan kwallon kafa na Indonesiya.

‘Yan sanda sun bayyana mamayar filin da aka yi a matsayin tayar da tarzoma, kuma sun ce an kashe jami’ai biyu, amma wadanda suka tsira sun zarge su da wuce gona da iri. Hotunan bidiyo sun nuna jami'an na yin amfani da karfi, suna magoya ‘yan kallon da sanduna, da kuma tura 'yan kallon baya.

Akalla jami'ai 11 ne suka harba barkonon tsohuwa - gwangwani takwas a cikin filin wasan, sannan uku kuma suka shiga filin don hana karin 'yan kallo sake shiga filin bayan tashi wasan.

Tawagar binciken da shugaban kasar Indonesia Joko Widodo ya kafa domin mayar da martani ga koke-koke da al'ummar kasar suka yi kan mace-macen da aka yi a kasar, ta kammala da cewa, hayaki mai sa hawaye ne ya haddasa yawaitar jama'a. Ya ce ‘yan sandan da ke bakin aiki ba su da masaniyar cewa an haramta amfani da hayaki mai sa hawaye a filayen wasan kwallon kafa da kuma yin amfani da shi ba tare da nuna bambanci ba a filin wasa, a tasha da wajen filin wasan, lamarin da ya sa ‘yan kallo sama da 42,000 da ke cikin filin wasa mai kujeru 36,000 suka yi gaggawar zuwa wuraren fita da dama daga cikinsu an kulle su.