Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na 2, ya bayyana rudanin da masarautar ta tsinci kanta a ciki sakamakon kawanyar da jami’an tsaro suka yiwa fadar Gidan Rumfa a makon da ya gabata.
A cewar Sarkin babu wata sanarwa a hukumance dangane da dalilin daukar matakin.
A jawabinsa yayin da yake karbar bakuncin wata tawaga daga Masarautar Bichi a yau Laraba, wacce ta zo domin nuna godiya da nadin sabon hakimin da aka yi musu, Munir Sunusi, Sarki Sanusi ya bayyana al’amarin da kokarin dauke hankalin da ba zai hana masarautar gudanar da ayyukan da ta sanya a gaba ba.
“Wannan al’amari da ya faru ba komai bane illa kokarin dauke hankula. Har yanzu bamu san dalilin afkuwar hakan ba, kuma wadanda al’amarin ya shafa basu bayyana dalilinsu na yin hakan ba. Sai dai, hakan ba za ta hana komai ba,” a cewar Sarkin.
Jami’an ‘yan sanda da takwarorinsu na DSS suka yiwa fadar kawanya a makon da ya gabata, inda suka takaita zirga-zirga daga ciki da wajen harabarta.
A yayin da hukumar tsaro suka yi shiru a kan lamarin, majiyoyi sun ce yiwa fadar kawanya baya rasa nasaba da nadin Munir Sanusi a matsayin Hakimin Bichi ko kuma wani shirin tattaunawa a kan kudurorin neman yin gyara a kan dokar harajin da suka janyo cece-kuce.
Gwamnatin jihar Kano ta caccaki gwamnatin tarayyar Najeriya game da lamarin, inda ta zargi hukumomin tsaro da wuce gona da iri.
Duk da halin rashin tabbas din da aka shiga, Sarki Sanusi II ya baiwa tawagar tabbacin ci gaba da gudanar da bikin nadin sabon hakimin kamar yadda aka tsara a wata rana a nan gaba.