Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa na nahiyar Afirka, yayi sanarwa ta musamman a yau Talata bayan hadari da aka samu inda mutum 8 suka rasa rayukan su, sama da talatin kuma suka jikkata a filin wasan Olembe a Yaoundé. Ana buƙatar kwamitin gaggawa don yin haske kan abin da ya faru" Inji Patrice Motsepe. Ya ƙara da cewa, za a fitar da rahoton binciken ne nan da ranar Alhamis.
Daga cikin matakin kuma ya ce wasan da aka shirya a Olembe ranar Lahadi mai zuwa, za a buga ne a filin wasa na omnisports Ahmadou Ahidjo.
Bayan cikakken rahoton kwamitin ne, ya ce za su iya yin la'akari da komawa ga Olembe. Har ila yau shugaban na CAF ya yi bayani cewa, alhakin tsaron taro na kan kwamitin shirya taron na gida, wato FECAFOOT da gwamnatin Kamaru.
Babu shakka wannan ranar Litini da ta gabata ta kafa mummunan tarihi, da mace mace daga cikin ‘yan kallon fafatawa tsakanin Kamaru da Comoros. Inda wasu 31 kuma suka jikkata a sanadiyar cinkoso da aka samu wajen shiga filin ƙwallon.
A cewar hukumomin lafiya, kusan mutum 31 ne suka samu raunuka, ciki har da wasu mutane biyu da suka karaya da kuma wasu biyu da ke fama da matsalar ƙoƙon kai. Hukumar CAF wacce ke shirya gasar fitattun kasashen nahiya Afirka, ta aika da babban sakatarenta asibitoti Yaoundé zuwa gefen waɗanda suka jikkata.
CAF ta ƙara cewa tana bincike a halin yanzu don samun ƙarin cikakkun bayanai kan yadda abubuwa suka faru.
Jami’ai sun kuma yi kokarin takaita mutanen da zasu je kallon wasa a filin mai daukar ‘yan kallo dubu 60 zuwa kashi 80 cikin dari saboda nuna damuwa a kan COVID-19.
Mun bukaci ƙarin bayani daga bakin jami'an tsaro na stade Olembé a wannan ranar, amma basu bamu amsa ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mohamed Ladan:
Your browser doesn’t support HTML5