Tun da farko Gwamnan jihar Arewa, Mijinyawa Bakari, ya kai wata ziyarar bazata yankin Waza tare da rufe wuraren aikin saran itatuwa da kona gawayi. Ya kuma bayyana damuwarsa kan illar da saran bishiyoyi babu kakkautawa ke yi ga muhalli.
Gwamna Bakari, ya zargi masu kudi ‘yan kasuwa da kasashen makwabta da ke zuba jari a wannan harka ta sayar da gawayi a matsayin makamashi.
Yayin ziyarar gwamnan ya ja hankalin shugabannin gargajiya da 'yan kwamitin saka ido da su kara azama wajen yakar wannan dabi’a.
Don kara zaburar da ma’aikatan da aka samar don cimma burin kare muhalli, gwamnatin kasar Kamaru ta samar da kayan aiki na tsaro saboda yadda ake ganin dan Adam ne ya fi gurbata muhalli tare da kone dazuka.
Domin karin bayani ga rahotan Mohamadou Rabiou: