Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Ya Haddasa Fargabar Matsalar Karancin Man Fetur A Wasu Sassan Amurka?


Shi dai bututun da masu kutsen suka toshe, shi ne mafi girma da ke ba gabashin Amurka kusan kashi 45 na man fetur da ake sha a yankin.

Sama da gidajen mai 1000 ne a kudu maso gabashin Amurka suka sanar da cewa mansu ya kare, saboda mamaye gidajen da masu ababen hawa suka yi, bayan fargaba da jama’a suka shiga ta yiwuwar samun karancin man fetur a kasar.

Jama’a sun yi ta garzayawa zuwa gidajen man ne, bayan da masu kutse ta yanar gizo, suka rufe wani makeken bututun man kasar.

Wannan matsala ta shiga rana ta shida kenan da aukuwa, abin da ya sa masu ababen hawa suka shiga fargabar mai yiwuwa a fuskanci matsalar karancin mai a nan gaba.

Hukumomi dai sun yi maza sun dauki matakan kare lafiya da muhalli a cewar kamfanin dillancin labarai na AP, ta hanyar hanzarta kai man da manyan motoci da jirgin ruwa ga masu bukata.

A gefe guda kuma sun y kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, domin ba za a fuskanci matsalar karancin man ba.

Shi dai bututun da masu kutsen suka toshe, shi ne mafi girma da ke ba gabashin Amurka kusan kashi 45 na man fetur da ake sha a yankin.

A ranar Juma’a masu kutsen suka shiga ta yanar gizo suka rufe shi, suka kuma nemi a biya su kudaden fansa kafin su bude su a cewar kamfanin dillancin labaran na AP.

Wannan hari, ya kara dasa alamar tambaya kan ingancin kariyar da kasar take da shi akan kayayyakin amfaninta na yau da kullum.

Sakatarorin makamashi da tsaron cikin gida sun kasance a Fadar White House a ranar Talata da yamma suna kokarin kwantarwa da mutane hankali, da bayar da gargadi a yayin da ake hasashen cewa farashin mai, zai yi tashin da ba’a taba ganin irinsa ba a kasar tsawon shekaru.

Jihohin Arewa da Kudanci da suka hada da Carolina da Tennessee da Georgia da kuma Virginia ne suka fi shafuwa daga tasirin rufe bututun da ke da tsawon kusan kilomita 9,000 kamar yadda rahotanni suka nuna.

XS
SM
MD
LG