Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalaman Fafaroma Benedict Na Karshe Kafin Mutuwarsa


Faithful pay homage to former Pope Benedict in St. Peter's Basilica at the Vatican
Faithful pay homage to former Pope Benedict in St. Peter's Basilica at the Vatican

A daidai lokacin da ake shirye-shiryen jana’aizar Fafaroma Benedict mai ritaya, an bayyana kalaman karshe da ya furta kafin komawarsa ga mahalacci.

"Ya Ubangiji, ina son ka," an ruwaito cewa su ne kalaman karshe da Fafaroma Emeritus Benedict ya furta, jim kadan kafin mutuwarsa, a cewar wani rahoto a shafin yanar gizo na Vatican News.

Sakataren Fafaroma mai ritaya, Archbishop Georg Ganswein, ya ce wata ma’aikaciyar jinya ce kadai ke tare da Benedict a lokacin.

"Ba na nan a lokacin, amma ma'aikaciyar jinya ta sanar da ni hakan jim kadan bayan faruwar lamarin," in ji Ganswein. "Wadannan su ne kalmominsa na karshe da ake iya fahimta, domin daga baya ya daina motsi."

Gawar Benedict za ta kasance a Basilica daga ranar Litinin zuwa Laraba, kuma za a yi jana'izarsa ranar Alhamis.

Benedict, shi ne Fafaroma na farko cikin shekaru 600 da ya sauka daga mukaminsa na fafaroma a fadar Vatican. Fafaroma mai ritaya ya rayu cikin wani gida dake bayan katangar Vatican kusan tsawon shekaru 10.

Yana da shekaru 95 a lokacin mutuwarsa.

XS
SM
MD
LG