Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guterres Ya Yi Tur Da Fadan Da Ke Faruwa Tsakanin Armenia da Azerbaijan


Dakarun Armenia da Azerbaijan, sun ci gaba da gwabza fada har zuwa rana ta biyu yau Litinin 28 ga watan Satumba a yankin Nagorno-Karabakh inda galibinsa kabilun Armenia ke zama, duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi na su kawo karshen fadan.

Bangarorin biyu sun zargi juna da yin amfani da manyan makamai.

Ma'aikatar tsaron Azerbaijan, ta ce sojojin Armenia sun yi barin wuta a garin Terter.

Yankin wanda ya balle, ya ba da rahoton cewa an samu karin akalla sojoji 15 da aka kashe, abinda ya sa adadin sojojin yankin da aka kashe tun daga ranar Lahadi zuwa yau ya zarta 30, lokacin da hukumomin yankin suka ce, Azerbaijan ta kai hari ta sama da kuma na manyan makamai.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya yi Allah wadai da kazamin fadan kuma ya bayyana takaicinsa kan "asarar rayukan da aka yi, da kuma yadda fadan ya shafi farar hula," a cewar wata mai magana da yawunsa a wata sanarwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG