A wata kuri'a mai cike da tarihi, Amurka da wasu kasashe 45 a kungiyar hana amfani da makamai masu guba, ko OPCW, sun tsaida shawara a taron membobin kungiyar tsaida shawar la'antar gwamnatin Bashar al-Assad a Siriya saboda ci gaba da amfani dakuma mallakar makamai masu guba. Irin waɗannan makamai sun keta alƙawari na Siriya a ƙarƙashin Yarjejeniyar taron dakile amfani da makamai masu guba ko CWC.
An zartar da shawarar ne tare da kasashe 87 da suka kada kuri'ar amincewa da ita sannan 15 kawai basu amince ba. Baya ga yin Allah wadai da amfani da makamai masu guba da Siriya ta yi, ta dakatar da wasu hakkoki da damar da Siriya ke da ita a karkashin yarjejeniyar - musamman ma 'yancinta na jefa kuri'a. Za a dawo da wannan 'yancin ne muddin babban daraktan OPCW ya ba da rahoton cewa Syria ta kammala wasu matakai. Misali, in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ned Price, “Dole ne Syria ta warware duk wasu matsaloli da suka shafi bayanan tarin makamai masu guba da shirinta.”
Kuri’ar ta biyo bayan fitowar wasu rahotanni biyu na binciken OPCW da Kungiyar tantancewa a cikin shekarar da ta gabata wanda a hukumance ya danganta gwamnatin Syria da harin makamai masu guba a shekarar 2017 da 2018. Wadancan rahotannin sun nuna cewa, Syria ta ci gaba da amfani da iskar gas mai guba a shekarun bayan da gwamnatin Assad ta yi watsi da amfani da su kuma ta mika su don halakarwa. Amurka kanta ta tantance cewa gwamnatin Asad ta yi amfani da makamai masu guba a kalla sau 50 tun lokacin da ta shiga CWC a 2013.
Wannan shine karo na farko da aka taba daukar irin wannan mataki akan wata kasa a OPCW. Mai magana da yawun kungiyar Price ya ce "Amurka na maraba da shawarar da OPCW ta yanke kuma tana jinjina wa gamayyar kokarin kasa da kasa na ci gaba da kiyaye ka'idojin kasa da kasa game da amfani da makamai masu guba."
"Amfani da makami mai guba a kowacce kasa na nuna barazanar tsaro da ba za a amince da ita ga kowa ba."