Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhaji Indimi Ya Gina Katafariyar Cibiyar Harakokin Kasuwanci A Amurka


Daga hagu zuwa dama Jeff Bush, Alhaji Indimi, Aliyu Modibbo da Aliyu Mustapha wanda ya dauki hoton a bikin bude cibiyar a Florida
Daga hagu zuwa dama Jeff Bush, Alhaji Indimi, Aliyu Modibbo da Aliyu Mustapha wanda ya dauki hoton a bikin bude cibiyar a Florida

An yi bikin bude cibiyar nazarin harakokin tattalin arziki da kasuwanci da zuba jari ta duniya mai suna Alhaji Muhammadu Indimi International Business Center

A ranar goma sha shida ga watan oktoba aka yi bikin bude ita wannan cibiya a jami'ar Lynn dake jahar Florida a nan Amurka.

Babban editan Sashen Hausa Aliyu Mustapha ne ya halarci bikin, sannan ya hada cikakken rahoto na musamman akan gina cibiyar daga farko har karshe.

Aliyu Musatpha ya tattauna da uban wannan tafiya wato Alhaji Muhammadu Indimi, da shugaban jami'ar Mr.Kevin Ross, da kuma Dr.Aliyu Modibo Umar tsohon ministan Abuja wanda ya samu gayyatar musamman domin ya halarci bikin bude cibiyar.

Ga rahoton na musamman da Aliyu Mustapha ya hada bayan ya halarci bikin bude cibiyar nazarin harakokin tattalin arziki da kasuwanci da zuba jari ta duniya mai suna Alhaji Muhammadu Indimi International Business Center a jami'ar Lynn dake jahar Florida a nan Amurka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:00 0:00
Shiga Kai Tsaye


XS
SM
MD
LG