Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Badakalar N432B: El-Rufa'i Ya Maka Majalisar Dokokin Kaduna A Kotu

Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai
Tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai

A yau laraba ne El-Rufa'i ya maka Majalisar Dokokin Kadunan a gaban babbar kotun tarayya dake jihar akan tauye masa hakkokinsa.

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya maka Majalisar Dokokin jihar a kotu akan ikirarinta na zargin cewar gwamnatinsa ta shekaru 8 ta wawure naira biliyan 432 inda ta bar jihar cikin dimbin bashi.

A yau laraba ne El-Rufa'i ya maka Majalisar Dokokin Kadunan a gaban babbar kotun tarayya dake jihar akan tauye masa hakkokinsa.

Tsohon gwaman Kaduna, Nasir El-Rufai
Tsohon gwaman Kaduna, Nasir El-Rufai

Karar wacce lauyan tsohon gwamnan, Abdulhakeem Mustapha, mai lambar Babban Lauyan Najeriya (SAN) ya shigar ta kalubalanci rahoton kwamitin majalisar wanda ya samu El-Rufa'i da laifin aikata almundahana.

Tsohon gwaman Kaduna, Nasir El-Rufai da lauyansa
Tsohon gwaman Kaduna, Nasir El-Rufai da lauyansa

A kunshin karar, El-Rufa'i ya bukaci kotun ta ayyana rahoton binciken majalisar a matsayin mara tushe kasancewar bai bashi damar kare kansa daga zarge-zargen da kwamitin ke yi masa tare da gwamnatinsa ba.

Wadanda ke cikin kunshin karar sun hada da Majalisar Dokokin Kadunan da antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG