Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yayin Da Sojojin Najeriya Ke Neman Daliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su, Iyaye Na Bukatar A Hanzarta Kubuto ‘Ya’yansu


‘Yan bindiga
‘Yan bindiga

A ranar Litinin din da ta gabata ne sojojin Najeriya suka fara farautar wasu masu garkuwa da mutane da suka yi awon gaba da daliban makaranta kusan 300 a jihar Kaduna kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana, yayin da iyayen dake cikin rudani suka bukaci a sanar da su lokacin sake haduwa da yaransu

WASHINGTON, D. C. - Majiyar ta ce rundunar One Division da ke Kaduna ce ke jagorantar aikin, kuma nan ba da jimawa ba za ta shawo kan ‘yan bindigan.

Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya
Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya

Majiyar ta kara da cewa sojojin sun samu goyon bayan jami’an ‘yan sanda, hukumar leken asiri da jami’an sojin sama, da kuma hukumar ‘yan banga ta jihar Kaduna, da ‘yan kato da gora wadda ta fi sanin yanayin yankin.

“Hukumomin tsaro da gwamnatin jihar suna aiki tukuru domin tabbatar da ‘yancin duk daliban da aka sace, muna samun ci gaba,” in ji Muhammad Shehu Lawal, mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

Sojojin Najeriya ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba a wannan lokaci.

Satar dimbim jama’a da aka yi a ranar Alhamis din da ta gabata, wanda shi ne na farko tun watan Yulin 2021, ya tarwatsa garin Kuriga mai nisan kilomita 90 daga babban birnin jihar Kaduna, inda iyaye ke bukatan hukumomi su kubuto da ‘ya’yansu.

Dakarun Najeriya Sun Yi Nasarar Kubutar Da Karin Biyu Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok
Dakarun Najeriya Sun Yi Nasarar Kubutar Da Karin Biyu Daga Cikin ‘Yan Matan Chibok

Kungiyar Boko Haram mai da’awar jihadi ce ta fara aiwatar da garkuwa da mutane a makarantu a Najeriya, inda ta kwashe dalibai sama da 200 a makarantar ‘yan mata da ke garin Chibok a jihar Borno shekaru goma da suka gabata. Inda wasu daga cikin ‘yan matan har yanzu ba a sake su ba.

Sai dai tun daga lokacin ne kungiyoyin masu aikata laifuka suka fara yin amfani da irin wannan dabara ba tare da wata alaka ko akida ba suka fara neman biyan kudin fansa, wanda da alama hukumomi na famar dakile yin hakan.

Satar mutane dai na tarwatsa iyalai da al’ummomin da suka hada ’yan jari-hujja don biyan kudin fansa, lamarin da ke tilasta wa iyaye sayar da dukiyoyin da suka fi daraja kamar filaye da shanu da hatsi domin a sako ‘ya’yansu.

Wadanda Suka Tsira Daga Masu Satar Mutane a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Wadanda Suka Tsira Daga Masu Satar Mutane a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Bala Ibrahim, daya daga cikin iyayen da aka sace ‘ya’yansu, ya ce babu wani karin bayani daga hukumomin yankin kan inda daliban suke.

“Abin da kawai muka sani ya faru tun bayan sace yaran shi ne an tura sojoji tare da toshe duk wata hanya da ta hada dajin Birnin-Gwari da jihar Zamfara,” kamar yadda Ibrahim ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.

"Sojoji suna cikin daji suna bin masu garkuwa da mutane."

A cewar wata cibiyar tuntuba ta SBM Intelligence da ke Legas, mutane 4,500 aka yi garkuwa da su a duk fadin Najeriya tun bayan hawan Tinubu mulki a watan Mayun da ya gabata.

Hoton masu satar mutane
Hoton masu satar mutane

Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce shugaban da ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro, har yanzu bai fito da wasu matakan ko hanyar yadda zai tabbatar da tsaro a Najeriya ba.

"Wannan lamarin na sace-sace na iya ci gaba har tsawon wannan shekara," in ji Ikemesit Effiong, shugaban bincike na SBM Intelligence.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG