Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aka Gudanar Da Sallar Idi A Makkah


Alhazai a Umrah
Alhazai a Umrah

A yau Litinin 2 ga watan Mayu al’ummar Musulmi daga fadin duniya, wadanda suka samu damar ziyarar kasar Saudiyya domin aikin Umrah a watan Ramadan, da ma ‘yan kasar, suka gudanar da Sallar Idi bayan shafe kwanaki 30 ana azumi.

Makkah, Saudiyya - Miliyoyin mutane ne suka hallarci Sallar Idi a garin Makkah a yau da ke zama daya ga watan Shawwal bayan hijirar Manzon Allah Muhammad SAW.

Wasu ‘yan Najeriya da suka yi nasarar samun wannan dama, sun bayyana farin ciki ganin ranar, musamman ma a kasar Saudiyya, duba da cewa shekaru biyu da suka wuce ba a sami damar yin aikin Umrah da Hajj ba saboda annobar coronavirus.

Sai dai wani abun mamaki shi ne yadda mutane suka yi saurin watsi da ka’idojin takaita yaduwar cutar COVID-19 a wannan rana ta wajen cudanya, wadda ita ce daya daga cikin hanyoyin da ake saurin kamuwa da cutar da aka yi fama da ita a kasashe da dama, ciki har da Saudiyya.

Wata ‘yar Najeriya da ta je Umrah ta yi addu’ar ganin karshen annobar COVID gaba daya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

XS
SM
MD
LG