Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke

Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke
Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke

Wata tawagar tsofaffin shugabanin kasar Benin ta kai ziyara Nijar domin tattaunar yiwuwar samar da maslaha a rikicin diflomasiyar da ya barke a tsakanin hukumomin mulkin sojan Nijar da gwamnatin jamhuriyar Benin sakamakon dambarwar da ta biyo bayan kifar da gwamnatin dimokradiya a watan Yulin 2023

Haka shine lamarin da ya yi sanadin rufe iyakokin kasashen biyu da kuma dakatar da ayyukan bututun da Nijar ke amfani da shi wajen fitar da manta zuwa kasuwannin duniya a karkashin wata yarjejeniyar da ta hada da China da Benin da Nijar din.

Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke
Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke

Ganin yadda rikici ke kara kamari a tsakanin hukumomin mulkin sojan Nijar da hukumomin makwabciyar kasa jamhuriyar Benin ya sa tsofaffin shugabanin kasar Benin, Nicephore Dieudonné Soglo da Thomas Yayi Boni, fara ziyara a Nijar da nufin tuntubar hukumomin kasar ta yadda za su zaunar da bangarorin biyu su fuskanci juna domin warware wannan rikici da ya yi sanadin rufe iyaka a tsakanin kasashen biyu.

Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke
Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke

Tuni dai tawagar ta yi ganawar farko da ministan cikin gida Janar Mohamed Toumba a jerin zaman da zai hada su da mukarraban gwamnatin mulkin sojan Nijar, kuma ana sa ran yiwuwar ganawarsu a nan gaba da shugaban majalissar CNSP Janar Tiani a fadarsa. Abin da wani masanin huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye ke alakanta shi da tasirin diflomasiya a yunkurin warware kowace irin takaddama.

Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke
Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Maslaha A Rikicin Diflomasiya Da Ya Barke

A baya hukumomin Nijar sun yi watsi da tayin sulhun da Benin ta zo da shi, inda Janar Abdourahamane Tiani ya ki ganawa da ministan da Patrice Talon ya turo dauke da wasikar biko a watan Mayun da ya gabata.

Amma masana na jan hankula a game da girman mu’amular kasashe a bisa tsarin tafiyar siyasar duniya.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Wata Tawaga Daga Benin Ta Kai Ziyara Nijar Domin Samar Da Masalaha A Rikicin Diflomasiyar Da Ya Barke.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG