Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Cuta Da Ba A Gane Kanta Ba, Ta Bullo A Sokoto


Gwajin cuta
Gwajin cuta

Yayin da cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya ke gudanar da bincike a kan wata cuta da ta bulla a Sakkwato, wadda ba a gane kanta ba, yanzu haka cutar na ci gaba da yaduwa .

A wannan ranar ta Alhamis ce dai ake sa ran babban daraktan cibiyar zai ziyarci Sakkwato don kara matsa kaimi ga binciken gano cutar da abin da ke kawo kamuwa da ita.

Tun a watan Maris da ya gabata ne aka samu bullar cutar, wadda ke kawo kumburin ciki da ciwon zuciya, a wasu yankuna na karamar hukumar mulkin Isa da ke gabashin Sakkwato, sai dai jami'an lafiya na yankin ba su kai rahoton bullar cutar ba, sai da aka kawo wasu da suka kamu da cutar a asibitin koyarwa ta jami'ar Usmanu Danfodiyo dake cikin birnin Sakkwato.

Kwamishinan lafiya ta jihar Sakkwato Asabe Balarabe ta nuna bacin rai a kan rashin sanar da bullar cutar har ta kama mutane talatin da biyu, inda daga baya gwamnati ta sanar da hedikwatar cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya don daukar matakin da ya kamata.

Cibiyar dai nan take ta aika da jami'anta domin gudanar da bincike, inda suka dauki samfurin abubuwa a yankunan da cutar ta bulla don bincike, sai dai kawo yanzu ba a kai ga gano abin da kawo cutar ba, acewar Dokta Nuhu Aliyu Dogon Daji, jami'i mai kula da yaduwar cututuka da annoba a jihar Sakkwato.

To sai dai duk da haka, jagoran ayarin kwararri masu kawo dauki na cibiyar hana yaduwar cututuka ta Najeriya Mr. Tajudeen Orowola, lokacin da yake yi wa mataimakin gwamnan jihar Sakkwato, Muhammad Idris bayani a kan cutar yace tuni sun tura dukan sanfurin da suka dauka a cibiyoyin gudanar da bincike a sassa daban daban kuma suna kan aikin binciken cutar.

A cewar sa da zaran sun kammala bincike suka bayar da rahoto za a san abinda kan kawo kamuwa da wannan cutar da kuma yadda za a shawo kan kamuwa da ita.

Zuwa yanzu dai cutar da ta bulla a karamar hukumar Isa, ta yadu zuwa makwabtan kananan hukumomi, a cewar jami'in kula da yaduwar cututuka da annoba, Dokta Nuhu Aliyu.

Dokta Nuhu Aliyu ya ce yau ne a ke sa ran babban daraktan cibiyar hana yaduwar cututuka ta kasa zai zo a Sakwwato domin karfafa guiwar aikin gano cutar da daukar matakan shawo kanta.

Sai dai wata matsala da masana suka ce tana addabar Najeriya kan gudanar da binciken cututuka ita ce rashin isassun wuraren bincike da ke da dukkan kayan aikin da ake bukata ga gudanar da bincike, abinda suke ganin akwai bukatar kara mayar da himma domin shawo kan wannan matsalar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG