A halin yanzu dai farashin kananzir, ya kai intaha a wasu jihihin kudu maso yammacin Najeriya, inda ake sayard da lita daya na kananzir, tsakanin Naira dari biyu da hamsi zuwa Naira dari ukku, wani wuri ma har fiya da haka, a maimakon Naira dari da ashirin (120) ko Naira dari da talatin (130).
Mafi yawan mutane suna amfani da kananzir, fiye da komai a wajen dahuwa, watar matar aure tace tsadar kananzir, yasa tilas tayi amfani da kadan daga cikin kudaden abinci domin siyan kananzir.
Shi kuwa shugaban ‘yan kasuwa, masu siyarda mai a jihar Oyo, Alhaji Abdulrahim Razak, yace suna sayarda man bisa la’akari da yadda suka siyo man ne, tunda yanzu babu man kananzir, tunda matattun mai a Najeriya, basu aiki.