Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salah, Klopp Sun Yi Musayar Kalamai

Salah, hagu, Klopp, dama (Ba a wannan wasan lamarin ya faru ba. Mun yi amfani da hoton ne don nuna misali.)
Salah, hagu, Klopp, dama (Ba a wannan wasan lamarin ya faru ba. Mun yi amfani da hoton ne don nuna misali.)

Ba a san dai mai ya janyo fadan ba, amma dukkan alamu sun nuna cewa kowa cikin bacin rai yake magana a hotunan bidiyon da aka nuna wasan na Liverpool da West Ham.

Burin Liverpool na ganin ta lashe kofin gasar Premier na bana ya kara dishewa bayan da ta tashi ci biyu da biyu da West Ham a wasan da suka kara a ranar Asabar.

Yanzu haka kungiyar ta Liverpool tana dingisawa don ganin ta kai ga gaci yayin da kocinta Jurgen Klopp ke shirin barin kungiyar a karshen wannan kakar wasa.

Liverpool ta yi nasara a wasa daya ne tak cikin wasanni biyar da ta buga a baya-bayan nan.

Salah na Liverpool a karawar da suka yi da West Ham inda aka tashi da ci 2-2
Salah na Liverpool a karawar da suka yi da West Ham inda aka tashi da ci 2-2

Wannan kunnen doki da kungiyar ta Liverpool ta yi da West Ham ya sa yanzu tana zaune a matsayi na uku a teburin gasar ta Premier.

Wani abu da ya kara fito da matsalar cikin gida da kungiyar take fuskanta shi ne musayar kalamai da aka yi tsakanin Mohamed Salah da kocins Klopp, lamarin da sai da dan Darwin Nunez ya shiga tsakaninsu a daidai lokacin da ake shirin yin canji ‘yan wasan.

Ba a san dai mai ya janyo fadan ba, amma dukkan alamu sun nuna cewa kowa cikin bacin rai yake magana a hotunan bidiyon da aka nuna wasan na Liverpool da West Ham.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG