Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Sayo Sabbin Jiragen Yaki 50


Rundunar sojin Najeriay ta ce za ta sayo sababbin jiragen sama 50, domin kara karfin ta na yaki da ‘yan ta’adda a yankin Arewa masu yamma na kasar.

A yayin da ya ke kaddamar da wasu sabbin sansanonin soji, da suka hada da wuraren ajiyar jiragen sama 2 a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, babban hafsan sojin sama na kasar, Air Marshal Hassan Bala Abubakar ya ce jiragen za su hada da masu saukar angulu 12 samfurin AH-1, da jiragen yakin soji 24 kirar M-346, da wasu jiragen komai da ruwanka 12 kirar AW-109, da kuma jirage 2 na jigilar sojoji.

Babban hafsan bai bayyana adadin kudin sayo jiragen ba, da kuma wanda zai kawo jiragen. To sai dai ya ce Najeriya na sa ran karbar jiragen ya zuwa shekara mai zuwa.

Hafsan Sojan Saman Najeriya, Air Marshal Hassan Bala Abubakar
Hafsan Sojan Saman Najeriya, Air Marshal Hassan Bala Abubakar

Abubakar ya ce za’a yi amfani da jiragen ne wajen kai hari kan ‘yan bindigar da suka addabi jama’a a jihohin arewa maso yamma da tsakiyar kasar a ‘yan shekarun nan.

To sai dai mai fashin baki kan lamurran tsaro Mike Ejifor, ya ce sayo jiragen sama 50 tamkar wuce goda da iri ne, kuma ta yiwu ba shi ne mafita ba.

Ya ce “na san hakan zai karfafa yaki da ta’addanci, amma ina da yakinin cewa kamata yayi mu maida hankali kan sojan kasa fiye da na sama. Ba yaki muke ba. Jiragen sama 50, akan wannan, haba kamata ya yi a maida hankali kan horar da sojojin kasa da kuma kula da jin dadinsu. Ina ganin da za mu fi samun sakamako mai yawa.”

Sanarwar ta Abubakar ta zo ne bayan wata sanarwa da hukumomin jihar Kaduna suka bayar a ranar Talata, ta hadin gwiwa da rundunar soji domin shirya wurare 3 na fagen dagar yaki da ‘yan ta da kayar baya a jihar, a cewar gwamnan jihar ta Kaduna Uba Sani.

Yace “mun yi matsaya da rundunar soji domin kafa sansanonin aiki a kudancin Kaduna, da wani a yankin Giwa da Birnin Gwari, Kuma ana nan ana kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata.”

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani

Rundunar sojin saman Najeriya ta fuskanci kakkausan suka a watan Disamban da ya gabata, bayan kashe mutane sama da 80 a wani harin jirgin sama a jihar Kaduna da aka auna gungun ‘yan bindiga. Wasu da dama kuma sun sami raunuka.

Hukumomin Najeriyar sun yi alkawarin kara yin taka-tsantsan domin kaucewa sake aukuwar irin wannan.

Ejiofor ya ce kamata yayi hukumomi su maida hankali kan inganta karfin sojin sama ta yadda za su iya samar da sahihan bayanai kan ayukan kungiyoyin ‘yan bindiga.

A yanzu dai masu fashin baki da ‘yan kasa masu kishi suna zuba ido domin ganin ko hukumomin za su kara yin taka-tsantsan, da kuma ko sabbin jiragen saman 50 za su yi wani tasiri wajen samar da tsaro a kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG