Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 21 Sun Mutu A Legas Sakamakon Kamuwa Da Cutar Kwalara


Cutar Kwalara A Kamaru
Cutar Kwalara A Kamaru

Adadin wadanda suka kamu da kwalara a fadin jihar ya karu zuwa mutum 401, inda cutar tafi kamari a yankunan Lagos Island da Kosofe da kuma Eti-Osa.

Mashawarcin gwamnan Legas na musamman akan harkokin kiwon lafiya, Dr. Kemi Ogunyemi, ta bayyana cewar adadin wadanda suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar, ya karu zuwa mutum 21, bayan rahotannin da aka samu a baya dake cewa mutum 350 ne suka kamu kuma 15 ne suka mutu.

Ta kuma kara da cewar adadin wadanda suka kamu da kwalara a fadin jihar ya karu zuwa mutum 401, inda cutar tafi kamari a yankunan Lagos Island da Kosofe da kuma Eti-Osa.

A yau Alhamis, Dr. Ogunyemi ta bayyana hakan lokacin da take bada karin haske game da annobar, bayan data gana da mambobin cibiyar bada agajin gaggawa a fannin kiwon lafiyar al’ummar jihar Legas.

Ta kara da cewar adadin wadanda cutar ta hallaka ya karu zuwa mutum 21, karin mutane 6 akan adadin da aka bada rahoto a baya.

A cewarta, an yi hasashen samun karuwar adadin sakamakon bukukuwan Sallar layya da aka yi, al’amarin dake janyo cunkoson jama’a a wuri guda.

Saidai tace, ana samun raguwar wadanda ke kamuwa da cutar a ilahirin kananan hukumomin jihar, musamman ma wadanda a da aka samu bullarta saboda daukar matakai da sanya idanu daga gwamnatin jihar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG