Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyini Agaji Da Jami’an Diflomasiya Sun Hadu A Paris Don Samar Da Agaji Ga Sudan


Taron kai agaji Sudan a Paris on Afrilu 15, 2024
Taron kai agaji Sudan a Paris on Afrilu 15, 2024

Manyan jami'an diflomasiyya da kungiyoyin agaji sun yi taro ranar Litinin a birnin Paris, domin bullo da hanyoyi na taimakon jin kai ga kasar Sudan da ke arewa maso gabashin Afirka, wadda ke daf da fuskantar matsananciyar yunwa, domin gudun sake fadawa cikin mawuyacin hali.

WASHINGTON, D. C. - Sudan ta fada cikin rikici a cikin watan Afrilun bara,lokacin da rikici ya barke tsakanin sojoji da dakarun sa kai ya barke a babban birnin Khartoum da sauran wurare a fadin kasar.

Firaiministan Sudan Abdalla Hamdok
Firaiministan Sudan Abdalla Hamdok

Shirin na neman agaji na Majalisar Dinkin Duniya, na bukatar kimanin dala biliyan 2.7 a wannan shekara domin samun abinci da kula da lafiya da sauran kayayyaki ga mutane miliyan 24 a Sudan, kusan rabin al'ummarta miliyan 51. Ya zuwa yanzu, masu ba da tallafin sun ba da dala miliyan 145 kawai, kusan kashi 5cikin 100, a cewar ofishin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka fi sani da OCHA.

Tun da farko dai Amurka da Saudiyya sun jagoranci yunkurin neman hanyar sasantawa da kawo karshen rikicin. Amma kokarin bai yi nasara ba, kuma tun a watan Oktoba rikicin ya samu koma baya saboda yakin Isra'ila da Hamas a Gaza, wanda ke barazanar fadada a yankin.

Wasu ‘yan Sudan da suka tsere Paris
Wasu ‘yan Sudan da suka tsere Paris

Ma'aikatan agaji, a halin da ake ciki, sun yi gargadin cewa Sudan na fuskantar bala'in yunwa mai girma, tare da yiwuwar mutuwar jama'a a cikin watanni masu zuwa. Hanyoyin samar da abinci da rarraba kayan abinci sun lalace kuma hukumomin agaji sun kasa isa yankunan da suka fi fama da bala'in.

Rahotanni da dama sun bayyana faruwar aikata laifuka na ta'addanci da suka hada da kashe-kashe da raba mutane da muhallansu da kuma fyade, musamman a yankin babban birnin kasar da kuma yammacin yankin Darfur.

Sudan Darfur
Sudan Darfur

Akalla kashi 37 cikin 100 na al'ummar da ke tsakiyar tashin hankali ko sama da haka suna fama da yunwa, a cewar OCHA. Kungiyar Save the Children ta yi gargadin cewa kimanin yara 230,000 da mata masu juna biyu da mata sabbin haihuwa za su iya mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki a watanni masu zuwa.

Kusan mutane miliyan 9 ne aka tilastawa barin gidajensu ko zuwa wurare masu aminci a cikin Sudan ko kuma zuwa kasashe makwabta, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG