Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Daure Bobrisky Bayan Daya Amsa Laifin Wulakanta Takardar Naira


Bobrisky
Bobrisky

 Alkali Abimbola Awogboro na Babbar Kotun Tarayya dake Ikeja ya aika da Idris Olanrewaju da aka fi sani da Bobrisky zuwa gidan gyaran hali bayan daya amsa laifin wulakanta takardar kudi ta naira.

WASHINGTON DC - Gabanin aikewa da shi zuwa gidan gyaran halin, Bobrisky ya cewa kotun bashi da masaniya game da dokar da ta haramta cin zarafin takardar Naira.

Saidai alkalin kotun ya yanke masa hanzari da cewar, babu uzuri ga rashin sanin doka.

Sashe na 21 (1) na dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta 2007 ya tanadi cewar, duk mutumin da aka samu da laifin jirkita yanayin kwandala ko takardar kudin Naira da CBN ya samar za'a iya zartar masa da hukuncin daurin da bai gaza watanni 6 ba ko kuma tarar da bata gaza naira dubu 50 ba ko kuma a hada masa dukka 2."

Sa'ilin da aka karanto masa laifinsa, Bobrisky yayi ikrarin aikata dukkanin tuhume-tuhume 4 dake da nasaba da wulakanta takardar naira.

Saidai gabanin a karanto tuhumar, lauyan Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, Suleiman Suleiman, ya bukaci kotun ta soke tuhuma ta 5 data 6 dake da nasaba da zarge-zargen halasta kudaden haram.

Daga bisani Mai Shari'a Abimbola Awogboro ya soke tuhuma ta 5 data 6.

Hakan ya share fagen gurfanar da bobrisky akan tuhuma ta 1 zuwa ta 4 da suka takaita ga zarge-zargen cin zarafin takardar naira.

Da safiyar Juma'ar nan ne, jami'an Hukumar EFCC suka taso keyar Bobrisky zuwa kotun da misalin karfe 9 da mintuna 12 na safiya cikin wata farar motar safa.

A ranar Larabar data gabata ne Hukumar EFCC ta cafke Bobrisky a bisa zarge-zargen cin zarafin takardar Naira da halasta kudaden haram.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG