Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karancin Kudi yana barazana ga yaki da zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika


Wani yana gwada maganin kashe zazzabin cizon sauro
Wani yana gwada maganin kashe zazzabin cizon sauro

Shugabannin nahiyar Afrika sun damu ganin gidauniyar yaki da malariya na bushewa

Shugabannin nahiyar Afrika sun damu ganin gidauniyar yaki da malariya na bushewa. Kungiyar hadin kan shugabannin kasashen nahiyar Afrika ta yaki da cutar zazazzabin cizon sauro da ake kira a takaice da turanci ALMA (African Leaders Malaria Alliance), da ta kunshi shugabannin kasashen nahiyar Afrika 41 da suka hada kai domin yaki da zazzabin cizon sauro a nahiyar, sun bayyana damuwa dangane da kudin da ake bukata na cimma wannan burin, da cewa, karancin kudi na barazana ga yunkurin.


Kungiyar ta bayyana cewa akwai gibin dala biliyan uku da miliyan dubu dari uku na kudin da ake bukata na aiwatar da dukan matakai da ayyukan yaki da zazzabin cizon sauro a nahiyar baki daya da ya hada da samar da magungunan farko karkashin shirin da ake kira a turanci a takaice ACTs, da gundanar da bincike da ake kira RTDs da kuma samar da gidajen sauro da dake dauke da magani-LLINs, daga yanzu zuwa shekarar 2015.


Shugabar kungiyar hadin kan shugabannin mai yaki da zazzabin cizon sauro Ellen Johnson Sirleaf ta Liberia ta ce “kanfen yaki da zazzabin cizon sauro ya tabbata hanyar nasarar inganta lafiyar mata da kananan yara saboda haka ba zamu kauda kai ba. Tilas ne mu cike gibin kudin yaki da cutar.”


Membobin kungiyar ALMA suka amince da yin amfani da kason da bankin duniya ya kebe domin gudanar da ayyukan bunkasa yankin wajen yaki da zazzabin cizon a da nufin cike wannan gibin.
Shugabannin sun kuma amince da daukar matakan gudanar da aikin a fili da kuma sa ido kan ci gaban da ake samu yayinda zasu dauki matakan da zasu taimaka wajen samun kudaden da za a yi amfani da su a fannin lafiya.
Kungiyar ta kuma yabawa kasashen Benin, da Burundi da Kamaru da Kenya da Mozambique da kuma Rwanda, sabili janye kudin fice kan kayayyakin da suka shafi yaki da zazzabin cizon sauro.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG