Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Mulkin Sojan Nijar Sun Zargi CEDEAO Da Yin Kafar Angulu Wa Shirin Sulhu


Taron manema labaran da Fira minista Lamine Zeine
Taron manema labaran da Fira minista Lamine Zeine

Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun zargi kungiyar ECOWAS da yi wa shirin sulhu kafar angulu bayan la'akari da yadda kungiyar ta yi nasam a zaman da ya kamata bangarorin su gudanar a yau 25 ga watan Janairun 2024 a birnin Yamai.

A bayannan da ya yi wa manema labarai cikin mintoci kalilan, Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine ya fara ne da zayyana yadda aka saka ranakun zama a na dagewa har sau biyu kafin daga bisani hukumomin mulkin sojan na Nijar da shugabanin kungiyar ECOWAS su ka cimma daidaito kan ranar 25 ga watan Janairun 2025 a matsayin wace za a fuskanci juna.

Sai dai an shafe tsawon wannan rana amma tawwagar jami'an kungiyar ba ta shigo ba in ban da Ministan Harakokin Wajen Togo, Robert Dussey, da ya sauka birnin Yamai inji Fira Minista Zeine.

Taron manema labaran da Fira minista Lamine Zeine
Taron manema labaran da Fira minista Lamine Zeine

Sai dai yunkurin jin ta bakin Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey wanda ya halarci taron maneman labaran da Firai Minista Lamine Zeinab ya kira ya ci tura.

Shugaban gwamantin rikon kwaryar ta Nijar ya bayyana wa manema labarai cewa bai zama dole ba ministan na Togo ya yi magana.

Taron manema labaran da Fira minista Lamine Zeine
Taron manema labaran da Fira minista Lamine Zeine

Rashin samun izinin sauka a filin jirgin saman Diori Hamani ita ce hujjar da Lamine Zeine ya ce kungiyar CEDEAO ta sanar a matsayin abin da ya hana jami'anta halartar wannan zama.

Da ma dai tun a jajibirin wannan zama wasu kungiyoyin kawancen Kungiyoyin Front Patriotique masu goyon bayan majalissarr CNSP suka tare a wurare akalla 3 a birnin Yamai da ke kan titi mai zuwa fadar shugaban kasa daga filin jirgi da nufin bayyana wa tawwagar da ECOWAS za ta turo cewa 'yan kasa ke da maganar kayyade wa'adin mulkin rikon kwarya.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG