Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Fidda Gargadi Kan Yiyuwar Ambaliya Yayin Da Kamaru Ke Sakin Ruwa Daga Madatsar Lagdo


Maiduguri, Satumba 10, 2024.
Maiduguri, Satumba 10, 2024.

A jiya Talata, gwamnatin tarayyar Najeriya ta gargadi al’ummar kasar game da ruwan da za’a saki daga madatsar lagdo dake kasar kamaru.

A cikin wata sanarwa, Shugaban Hukumar kula da kogunan Najeriya, Umar Muhammad, yace za’a fara aikin sakin ruwan cikin tsari a ranar 17 ga watan Satumbar da muke ciki.

A cewar sanarwar, ana sa ran yawan ruwan da za’a sakin ya karu matuka cikin kwanaki 7 masu zuwa gwargwadon kwararowar ruwa daga kogin Garwa.

Saidai shugaban kula da kogunan Najeriyar, yace babu wani abun tada hankali game da hakan.

Umar Muhammad ya kara da cewar, “da babbar murya hukumarmu ke tabbatar da cewa babu wani abun daga hankali kasancewar ba’a tsammanin samun wata gagarumar ambaliya a gangaren kogunanmu na Najeriya kasancewar har yanzu yawan ruwan dake gudanawa a kogin benuwe bai haura ka’ida ba.”

“Duk da haka, yana da matukar muhimmanci ga dukkanin jihohin suka kogin Benuwe ya ratsa ta cikinsu, da suka hada da: Adamawa da Taraba da Benuwe da Nasarawa da Kogi da Edo da Delta da anambra da Bayelsa da Cross River da Rivers da ilahirin matakan gwamnatoci 3 (tarayya da jjihohi da kananan hukumomi) su tsaurara sa idanu tare da aiwatar da matakan tunkara da takaita yiyuwar samun ambaliya, a hakika tana iya afkuwa sakamakon samun karin tumbatsa a manyan kogunanmu a irin wannan lokaci”, a cewarsa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG