Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Borno Ta Bude Sansanin Ajiye Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa


'Yan gudun hijira da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Maiduguri (Hoto: Facebook/Rariya)
'Yan gudun hijira da ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a Maiduguri (Hoto: Facebook/Rariya)

Yankunan da ambaliyar ta shafa sun hada da Shehuri, wasu sassa na Yankin G.R.A., Gambomi, Budum, Bulabulin, Adamkolo, Wurin Millionaires, Kasuwar Litinin da Gwange a cewar hukumar ba da agajin ta gaggawa.

Gwamnatin Jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya ta bude sansanin ‘yan gudun hijira na Bakassi wanda zai zama mafaka ga wadanda mummunar ambaliyar ruwa ta shafa.

Da tsakar daren Litinin wayewar garin Talata, mazauna birnin na Maiduguri suka fuaskanci mummunar ambaliyar ruwa.

Lamarin ya faru ne bayan da wani sashe na madatsar ruwan Alau ya fashe ya haddasa kwarara ruwa zuwa unguwannin da ke kusa.

Wuraren da abin ya shafa sun hada da Shehuri, wasu sassa na Yankin G.R.A., Gambomi, Budum, Bulabulin, Adamkolo, Wurin Millionaires, Kasuwar Litinin da Gwange a cewar hukumar ba da agajin ta gaggawa.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun kakakinsa Bayo Onanuga, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa al’umar jihar ta Borno kan wannan ibtila’i.

“Shugaba Tinubu ya ba gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum tabbacin cikakken goyon baya wajen tallafawa wadanda lamarin ya tutsa da şu.”

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima wanda dan asalin jihar ta Borno ne, ya kai ziyarar birnin na Maiduguri don jajanta wa al’uma inda ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta yi maza-maza ta mayar da mutane gidajensu.

Kuma tuni har ya ba hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta ba da umarnin kai dauki birnin na Maiduguri.

NEMA ta ce tana aiki tare da Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno wajen samar da taimakon jin kai ga wadanda ke cikin damuwa a sansanin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG