Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Rasa Muhallansu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Ghana

Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Kimanin mutum 20,000 ne ibtila'in ambaliyar ruwa ta tilastawa barin gidajensu a yankin kudu maso gabashin kasar Ghana da wasu matsugunai a birnin Accra da ma jihar gabashin kasar.

KUMASI, GHANA - Wannan matsala dai ta samo asali ne sakamakon ambaliya da madatsar ruwa ta Akosombo da ke samarma kasar wutan lantarki ta haifar, wanda ya yi sanadin lalata gidaje da gonaki da ke gabar kogin Volta.

Ambaliyar ta haifar da katsewar ayyuka masu muhimmanci, inda wasu yankunan suka rasa ruwan sha da wutar lantarki.

An kuma rufe makarantu tare da cibiyoyin kiwon lafiya da dai sauransu.

Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Mataimakin shugaban kasar Ghana Dr. Mahmud Bawumia ya shaidawa al’ummar yankin da wannan iftiai ya rutsa da su yayin da ya gabatar da ziyara a yankin cewa wannan ibtala'in shi ne mafi muni da kasar ta taba fuskanta tun shekarar 1963.

Kafin ambaliyan kuwa, hukumar kula da kogin Volta ta gargadi mazauna a yankin da su koma wani wuri na daban amma kuwa jinkirin wajen sauya matsuguni ya janyo barnata dukiya masu yawa a cewar alkalumma.

Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Abin fargaba a yanzu shi ne hukumar bincika yanayi ta kasar Ghana ta yi hasashen cewa an ci gaba da tafka ruwan sama mai karfi fiye da wanda aka shaida yanzu a yankunan da wannan al'amari ya shafa.

Domin ganin ba a fuskanci matsala makamancin haka nan zuwa gaba ba wata cibiyar da ke baiwa gwamnatin Ghana shawara kan sauyin yanayi tare da samar da abinci wato Centre For Climate Change and Food Security ta bukaci da gwamnatin kasar ta dau matakan fadada matsadan ruwa ta Akosombo Dam da sauya ma mazauna wannan yanki matsuguni.

Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa
Durban Mutane Suka Rasa Matsugunansu A Ghana Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Tuni wasu kungiyoyin ba da agaji da ma gwamnati suke ba da tallafi ga wadanda wannan al'amarin ya shafa ciki har da matakin taimakon manoma da kimanin miliyan arba'in na dalan Amurka da gwamnati ta dauka.

Sai dai ba wannan masifar ambaliyar ta madatsan ruwan Akosombo kadai ke addaban al’ummar Ghana ba har da na madatsan ruwa ta Bagre Dam na kasar Burkina Burkina wanda ke tilasta ficewar dubban mutane a yankunan arewa mai nisan kasar.

-Hamza Adam

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG