Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BABBAR SALLAH: Gwamnati Ta Ba Ma’aikata Hutun Laraba Da Alhamis A Najeriya


Masu sallar Eidi
Masu sallar Eidi

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba ma’aikata hutun ranaku Laraba 28 da Alhamis 29 domin ba al’umma Musulmi damar gudanar da shagulgulan babbar sallah.

A ranar Laraba ne za a gudanar da sallar Idi a fadin kasar, kamar a sauran kasashe, bayan an gunadar da Arfat a ranar Talata.

Sanarwar hutun ta na kunshe ne a cikin wata takarda da babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida na gwamnatin tarayyar Oluwatoyin Akinlade ya fitar.

A cikin sanarwar, Akinlade ya taya al'ummar Musulmi a cikin kasar da ma duniya baki daya murnar bikin na babbar sallah.

Gwamnatin Najeriya ta kuma bukaci al’ummar Musulmi da daukacin ‘yan Najeriya da su rungumi sadaukarwa domin cigaban al’ummarsu da kasa baki daya.

Sallar layya na da matukar muhimmanci a addinin Musulunci. Rana ce da ke tunatar da daukacin al’ummar Musulmin duniya irin sadaukar war da Annabi Ibrahim ya yi da dansa Isma’il domin yin biyayya ga Allah, a inda Allah ya fanshi annabi Isma’il da rago daga Aljanna kamar yadda yazo a tarihin musulunci.

Al’ummar musulmi a fadin duniya na gudanar da bukukuwan wannan rana ta hanyar halartar salloli na jama’a, da cin abinci mai dadi, da raba naman hadaya ga masu karamin karfi.

Wannan biki ya kasance wata dama ce ga musulmi wajen zurfafa imaninsu da karfafa dankon zumunci da ‘yan uwantaka.

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar hukumomin da abin ya shafa za su dauki matakan da suka dace don ganin an gudanar da bukukuwan ranar hutu cikin kwanciyar hankali.

Wannan ya hada da hada kai da matakan tsaro domin wanzar da zaman lafiya da zaman lafiya a lokutan bukukuwan.

A karshe gwamnatin ta jaddada kudirinta na karfafawa 'yan kasa gwiwa da su rungumi hadin kai a matsayin ginshikan cigaba.

~ Yusufdeen Aminu

XS
SM
MD
LG