Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Senegal


Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall

Ana gudanar da zaben ne makonni bayan da shugaba Macky Sall ya yi kokarin jan lokacin zaben har zuwa karshen shekara, hakar da ta ka sa cimma ruwa.

A ranar Lahadi 24 ga watan Maris na shekarar 2024 ne aka bude rumfunan zabe a Senegal a zaben shugaban kasa mai cike da rudani, wanda ya biyo bayan rashin tabbas na tsawon watanni da tashe-tashen hankula da suka shammaci kasar dake yammcin Afirka, a matsayin tabbataccen tsarin dimokuradiyya a yankin da ya fuskanci juyin mulki a shekarun baya.

Tun da sanyin safiya ne tituna suka kasance ba kowa a babban birnin kasar Dakar, an kuma jibge jami’an ‘yan sanda a cikin motoci masu sulke a ko'ina a birnin. A wajen rumfunan zabe, ‘yan sanda sun duba katunan zabe yayin da jama’a maza da mata suka jeru akan layi.

An gudanar da zaben ne makonni bayan da shugaba Macky Sall ya yi kokarin jan lokacin zaben har zuwa karshen shekara, hakar da ta ka sa cimma ruwa. An hana Sall tsayawa takara karo na uku saboda kayyade wa'adin tsarin mulki. A saboda haka ne ake kada kuri'a a cikin watan Ramadan, wata mai alfarma da musulmi ke azumi tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Zaben dai na shirin zama karo na hudu da al'ummar kasar za ta mika mulki ga dimokuradiyya tun bayan da kasar ta Senegal ta samu 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG