Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kwato Naira Biliyan 30 Kuma Ana Binciken Asusu 50 Na Banki A Badakalar Betta Edu - EFCC


Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja
Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja

Tun a watan Janairu ne aka dakatar da Ministar Harkokin jinkai da yaki da fatara, Betta Edu, bisa zargin karkatar da kudaden jama’a da suka kai dalar Amurka 640,000 zuwa asusun banki na sirri.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kwato ma Gwamnatin Tarayya Naira Biliyan 30, yayin da ta kuma sanya asusun ajiyar banki 50 a jerin abubuwan da ake bincike a ci gaba da binciken tsohuwar Ministar Harkokin Jinkai da Yaki da Fatara, Betta Edu, ciki har da tsohuwa Jami’ar zartarwa na Hukumar Kula da Zuba Jari ta Kasa (NSIPA), Halima Shehu da aka dakatar.

Tun a watan Janairu ne aka dakatar da ministar harkokin jinkai da yaki da fatara Betta Edu bisa zargin karkatar da kudaden jama’a da suka kai dalar Amurka 640,000 zuwa asusun banki na sirri.

BETTA EDU
BETTA EDU

Nan take shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Edu da Shehu saboda zargin karkatar da kudaden. Shugaban ya kuma dakatar da shirin na Social Investment, sannan ya bukaci hukumar EFCC da ta dauki nauyin lamarin tare da bincike jami’an da ke da hannu a ciki.

A lokacin Dr Edu mai shekaru 37 ta musanta aikata laifin. Ofishinta ya ce ta amince da tura kudin zuwa wani asusu na sirri, wanda ba a sunanta ba, amma ta ce an yi hakan ne don aiwatar da tallafi ga marasa galihu.

Halima Shehu
Halima Shehu

Bayan watanni uku, shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, wanda ya bayyana haka, ya ce hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na samun ci gaba a binciken, inda ya jaddada girman lamarin da kuma bukatar ‘yan Najeriya su yi hakuri.

Shugaban Hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana haka a cikin sabuwar mujallar hukumar mai suna EFCC-Alert inda ya ce:

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede
Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede

“Mu na da dokoki da ka’idoji da ke jagorantar bincikenmu. ‘Yan Najeriya ma za su san cewa tuni aka dakatar da su kuma hakan ya samo asali ne daga binciken da muka yi, kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa a shirye yake ya yaki cin hanci da rashawa.

Bugu da kari, dangane da wannan lamari, mun kwato sama da Naira biliyan 30, wadanda tuni ke cikin asusun gwamnatin tarayya. Yana ɗaukar lokaci don kammala bincike; mun fara wannan lamari ne kasa da makonni shida da suka gabata. Akwai lokuta da ake ɗaukar shekaru ana bincike. Akwai kusurwoyi da yawa a gare shi. Mu kuma akwai bukatar mu bi ta da wasu binciken da muka gani. Ya kamata ‘yan Nijeriya su ba mu lokaci kan wannan al’amari; muna da ƙwararru akan wannan harka kuma suna buƙatar yin abubuwa daidai."

A cikin jawabin da ya yi, shugaban ya cigaba da jaddada cewa a yanzu haka hukumar na bincikar asusun banki sama da guda 50 da hukumar ta gano akwai kudade a ciki, yana mai cewa lallai hukumar EFCC bata dauki wannan aiki da wasa ba kuma suna nan suna aiki tukuru duk da irin yawan aikace-aikace da ke kansu bayan wannan.

Shugaban EFCC ya ba da tabbacin cewa:

"Mun bankado tabargaza da yawa da muka gano yayin bincikenmu. Idan batun burin ganin masu laifi a gidan yari ne, dole a kara hakuri mu bi tsarin da ya kamata na doka" in ji shi.

Bugu da kari, shugaban na hukumar EFCC ya bayyana cewa kudaden da aka kwato sun riga sun shiga asusun gwamnatin tarayya, sa’annan ya ce yayi imanin cewa a yanzu haka ‘yan Najeriya sun fara ganin tasirin aikin hukumar ya zuwa yanzu.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG