Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Sojan Da Ya Harbe Wani Matashi Har Lahira A Zaria


Shugaban rundunar sojin Najeriya, Janar Taoreed Abiodun Lagbaja
Shugaban rundunar sojin Najeriya, Janar Taoreed Abiodun Lagbaja

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Darektan yada labaran rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya ce ana kan gudanar da bincike kan kisan matashin mai suna Ismail Muhammad.

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana tsare da sojan da ake zargi da harbe wani matashi har lahira a yankin Samaru da ke Zaria a jihar Kaduna.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Darektan yada labaran rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya ce ana kan gudanar da bincike kan kisan matashin mai suna Ismail Muhammad, lamarin da ya faru a ranar Talata.

Sanarwar ta kara da cewa Shugaban rundunar sojin Najeriya Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ya tura wata babbar tawaga karkashin jagorancin Babban Kwamandan runduna ta 1, Manjo Janar Lander Saraso zuwa gidan mamacin don yi musu ta’aziyya.

“A ranar 6 ga watan Agusta, sojojin Najeriya sun samu labarin cewa wasu bata-gari sun taru a yankin Samaru suna kona tayu akan hanya suna kuma jifan jami’an tsaro.

“Da zuwan su, sai bata-garin suka fara yunkurin kai wa sojojin hari, lamarin da ya sa sojan ya yi harbin gargadi, kuma abin takaici harbin ya samu wani yaro mai shekaru 16 da ake kira Ismail Muhammad. Tuni mun kama sojan ana kuma gudanar da bincike.” Sanarwar ta ce.

Sai dai kamar yadda rahotanni suka nuna, wasu mazauna unguwar ta Samaru sun musanta labarin da sojin na Najeriya suka bayar, suna masu dasa alamar tambaya kan yadda harbin gargadi da ya kamata a ce sama aka yi shi ya samu Muhammad.

Najeriya ta shiga kangin zanga-zanga tun a aranar 1 ga watan Agusta inda jama’a suka fit akan tituna don nuna korafinsu kan yanayin tsadar rayuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG