Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Taron Kasashen Afirka Don Neman Hanyar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa


Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana
Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana

An kiyasta cewa ana samun asarar dala tiriliyan 3.6 a tattalin arzikin duniya a shekara, a sanadiyar harkokin da suka danganci cin hanci da rashawa.

ACCRA, GHANA - Hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun yi gargadin cewa lamarin na bukatar kulawa cikin gaggawa domin tabbatar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a kasashe masu tasowa.

Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana
Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana

Hakan ya bayyana ne a taron shekara-shekara na shugabannin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka dake kungiyar Commonwealth karo na 14 dake gudana a birnin Accra na kasar Ghana.

Shugabannin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa daga kasashe 21 a Afirka, na kungiyar kasashen Commonwealth na gudanar da taron kara wa juna sani a birnin Accra, da nufin karfafa yaki da cin hanci da rashawa a yankin.

Sakatariyar kungiyar Commonwealth ce ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin Ghana kuma taken taron na bana shi ne: "Ƙarfafa Cibiyoyi da Tabbatar da Gaskiya: Hanyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Afirka ta Commonwealth".

Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana
Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana

Mataimakin babban sakatare a sakatariyar Commonwealth, Farfesa Luis Francheshi, ya jaddada illar cin hanci da rashawa ga ci gaban Afirka, musamman idan aka yi la’akari da albarkatu da dukiya da ke cikin nahiyar.

“Asarar da aka yi kan hanci da rashawa a duniya ya kai dala tiriliyan 3.6 a shekara. Kuma ba shakka ba za a iya yin bayanin yadda kashi 40% na albarkatun ma'adinai na duniya suka kasance a Afirka; da damarmaki masu yawa; da tarin makamashi; da yawan matasa; amma kuma a zahiri ba a ambatarmu idan ana batun masu ci gaban tattalin arziki a duniya, da kudaden shiga na GDP, da kuma ci gaba. Ina hankoron wadancan manyan shugabannin da suka kafa Afirka?

Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana
Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana

Kamar yadda Babbar Sakatariyar kungiyar Commonwealth, Rt Hon Patricia Scotland KC ta ce: “Afirka na asarar sama da dala biliyan 50 a duk shekara saboda safarar kudi ta haramtacciyar hanya. Hakika, a cikin shekaru 50 da suka gabata, asarar da Afirka ta yi ga cin hanci da rashawa ta zarce adadin duk wani taimakon raya kasa da aka samu a wannan lokacin”.

Antoni Janar kuma ministan shari’a na Ghana, Godfred Yeboah, wanda ya wakilci shugaban kasa, Nana Akuffo-Addo ya ce gwamnatinsu ta aiwatar da matakan dakile cin hanci da rashawa.

Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana
Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana

Gwamnatin Nana Addo Dankwa Akufo Addo a shekarar 2019 ta jagoranci zartar da dokar kare hakkin bayanai, wato doka ta 989.

Ya ce, gwamnati ta karfafa hakan ne domin muhimmancin samun labarai da yada shi ba da tsangwama ba, wurin yaki da cin hanci da rashawa.

Lauya Anas Mohammed, mai yaki da cin hanci da rashawa, ya ce cin hanci da rashawa na cikin lamarin dake mayar da kasa baya. Ya kara da cewa, Idan an karfafa hukumomin yaki da rashawa, kuma aka aiwatar da dokokin yaki da rashawan, in hakan bai taimaka wurin dakile lamarin ba, to hakika zai rage.

Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana
Taron kasashen Afirka akan cin hanci da rashawa a Ghana

Taron, wanda za kammala a ranar 11 ga watan Mayu 2024, ya hado kan mambobin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Commonwealth a Afrika, da manyan jami'an gwamnati, da kungiyoyin kasa da kasa, kungiyoyin farar hula, da masu tsara manufofi, don a tattauna illar cin hanci da rashawa ga ci gaba mai dorewa a Afirka, da kuma gano sabbin hanyoyin yaki da lamarin da ya addabi nahiyar.

Saurari Cikakken Rahoto Daga Idris Abdullah:

An Gudanar Da Taron Kasashen Afirka Don Neman Hanyar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG